Hajji: An Sauke Farali, Sahun Farkon Alhazan Kano na Hanyar Dawowa Gida Daga Saudi
- Bayan kammala ibadar aikin hajjin bana, wasu daga cikin alhazan Kano sun kama hanyar dawowa gida a yau Talata
- Jiigin farko na alhazan zai dauko alhazai 554 da suka fito daga kananan hukumomin Gwale, Dala, Ungogo da kuma Fagge
- Babban daraktan hukumar alhazai ta Kano, Lamin Rabi’u Dan Baffa ya bukaci mahajjatan da su ci gaba da ayyuka na gari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano- Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ce a yau Talata jirgin farko dauke da wadanda su ka kammala aikin hajjin bana za su iso gida.
Jirgin na dauke da wasu daga cikin alhazan da suka fito daga kananan hukumomin Gwale, Dala, Ungogo da kuma Fagge.
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa jirgin zai taso da alhazai 554 daga filin jrgin saman Sarki Abdul’azeez dake birnin Jeddah na Kasar Saudiyya kai tsaye zuwa Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alhazan Kano sun yi bankwana da Saudiyya
Babban daraktan hukumar alhazai ta Kano, Lamin Rabi’u Dan Baffa yayin da ya yi bankwana da wasu alhazai a yau ya ce alhazan za su fara dawowa gida.
Lamin Dan Baffa wanda ya samun wakilcin daraktan hukumar mai kula da aikin hajji, Kabiru Muhd Panda, ya bukaci alhazan da su kyautata mu’amalarsu da jama'a.
Hajj Reporters ta wallafa cewa babban darktan ya ce idan sun dawo gida, su ci gaba da aikata ayyukan alheri irin wanda suka yi tun daga farkon hakkin hajji har zuwa karshensa.
Dan Baffa yace hukumar sa zata ci gaba da jigilar alhazan har ya zuwa ranar da za’a kammala dawo da su gida Kano.
Alhaji ya mayar da kudin tsintuwa
A baya mun ruwaito cewa wani Alhajin Najerya ya kankaro darajar kasarsa bayan ya mayar da wasu makudan kudi da ya tsinta a Makkah.
Shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), Malam Jalal Ahmad Arabi ya yabawa mahajjacin da ya fito daga jihar Jigawa bisa hali na gari da ya nuna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng