Ana Gyara Gini Ya Ruguzowa Bayin Allah a Abuja, Mutane Sun Samu Raunuka

Ana Gyara Gini Ya Ruguzowa Bayin Allah a Abuja, Mutane Sun Samu Raunuka

  • Rahotanni sun nuna cewa an samu rushewar wani gini da ake yiwa kwaskwarima a birnin tarayya Abuja a yammacin jiya Litinin, 1 ga watan Yuli
  • Kakakin rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin tare da karin haske ga manema labarai
  • Josephine Adeh ta kuma bayyana yadda labarin ya zo musu da kuma matakin da suka dauka cikin gagggawa musamman kan wadanda abin ya shafa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An samu mummunan haɗari yayin da wani gini ya rufta kan mutane a birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa hadarin ya jikkata wasu mutane yayin da ginin ya zubo masu a yammacin jiya.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mutane sun mutu yayin da ginin katafaren Otal ya rufta a Abuja

Abuja
Rushewar gini ya jikkata mutane uku a Abuja. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kakakin rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗanda gini ya ruso kansu a Abuja

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa ginin ya ruso ne a lokacin da wasu mutane da ake tunanin suna aiki a wajen ke cikin zagayen ginin.

Sai dai hukumomi sun tabbatar da cewa mutane uku ne kawai suka samu raunuka yayin da ginin ya ruso.

Rahotanni sun yi nuni da cewa ginin ya ruso ne a yammacin jiya Litinin da misalin karfe 4:40 da dare, rahoton Channels Television.

Bayanin yan sanda kan ruguzowar ginin

Kakakin rundunar yan sandan birnin tarayya, Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce babu wanda ya rasu.

Sai dai rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa akwai mutane uku da suka jikkata kuma an tafi da su asibiti domin samun kulawa.

Kara karanta wannan

Kishin ƙishin din kara kudin fetur ya jawo kulle gidajen mai, jama'a sun shiga tasko

Rundunar ta bayyana cewa sun yi sauri domin tafiya wurin a lokacin da suka samu kiran gaggawa kan haɗarin.

An kashe 'yan fashi a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja tace an fafata tsakanin jami'an tsaro da 'yan fashi a karamar hukumar Abaji.

Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, CP Benneth Igweh, ya ce an yi nasarar kashe 'yan fashi biyu a yayin fafatawar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel