Yan gida daya su 6 sun mutu bayan gini ya ruso masu a Kebbi

Yan gida daya su 6 sun mutu bayan gini ya ruso masu a Kebbi

- Labari da muke samu ya nuna cewa uba, uwa da yaransu hudu sun mutu a lokaci guda a yankin Yaldu da ke karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi

- Hakan ya afku n bayan gidan da suke ciki ya rushe sakamakon ruwan sama da aka shafe kwanaki ana yi

- Tuni dai aka binne su daidai ta koyarwar addinin Islama

Rahotanni da muke samu ya nuna cewa yan gida daya su shida da suka hada da uba, matarsa da yaransu hudu sun mutu.

Mummunan al’amarin ya afku ne sakamakon rushewar gidan da suke ciki a yankin Yaldu da ke karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi.

A bisa ga rahotanni, ginin ya zube ne bayan shafe tsawon kwanaki da dama ana zuba ruwan sama a yankin.

Iyalan wadanda ke cikin gidan a lokacin da ya rushe duk sun mutu, shafin Linda Ikeji ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Dangin miji sun fatattaki mata saboda ta nemi hakkin yarta mai shekaru 8 da aka yi wa fyade

Tuni dai aka binne su bisa ga koyarwar addinin Islama.

Ga hotunan su a kasa:

Yan gida daya su 6 sun mutu bayan gini ya ruso masu a Kebbi
Yan gida daya su 6 sun mutu bayan gini ya ruso masu a Kebbi
Asali: Twitter

Yan gida daya su 6 sun mutu bayan gini ya ruso masu a Kebbi
Yan gida daya su 6 sun mutu bayan gini ya ruso masu a Kebbi
Asali: Twitter

A wani labarin, hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Jigawa, SEMA, ta sanar da cewa yawan mutanen da suka mutu ya kai 2 tare da dubban gidaje da gonakin da suka lalace sakamakon gagarumar ambaliyar da ta auku a jihar.

Sakataren hukumar, Mr Yusuf Sani Babura, ya sanar wa manema labarai a Dutse cewa ambaliyar, wanda ke aukuwa duk shekara, ya shafi 17 daga cikin kananan hukumomi 27 na jihar wanda hakan ya jefa rayukan jama'a mazauna garuruwan cikin rudani.

Ya kara da cewa mafi yawar wanda suka rasa rayukan su yara ne kanana sakamakon rugujewar gine gine.

Ya ce haka; "Ambaliyar da ta saba aukuwa duk shekara ta halakar da gidaje 5,000 gonaki da yawa kuma sun nutse inda amfanin gona daya hada da su masara, gero, dawa da shinkafa suka lalace a kananan hukumomi da yawa da ke jihar sakamakon gagarumar ambaliyar ruwan data auku a satin daya gabata".

KU KARANTA KUMA: Mace mai idon mage: Uwargidar gwamna ta karbarwa ma’auratan hayar katafaren gida

A cewar sakataren, gwamantin jihar ta bawa hukumar SEMA umurnin ta gaggauta samar da taimako ga garuruwan da abun ya shafa. "an tanadar da wurin na wucin gadi ga wadanda abun ya shafa wanda ya hada da makarantu, masallatai da kuma gidajen 'yan uwa".

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng