Ana Cikin Matsalar Abinci, Sarkin Katsina Ya Shiga Sahu, Ya Jagoranci Sallar Roƙon Ruwa

Ana Cikin Matsalar Abinci, Sarkin Katsina Ya Shiga Sahu, Ya Jagoranci Sallar Roƙon Ruwa

  • Sarkin Katsina, Mai martaba Abdulmimin Kabir Usman ya jagoranci dubban jama'a zuwa yin sallar roƙon ruwa
  • Hakan yana zuwa ne yayin da ake tsaka da matsalar tsaro da ƙaruwar farashin kayan masarufi a kusan duk Najeriya
  • Limamin babban masallacin jihar, Imam Gambo Mustapha ne ya yi limanci a filin idin jihar Katsina a ranar Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - A ƙoƙarin shawo kan matsalar abinci da rashin tsaro da suka addabi Katsina, Sarkin Katsina, Abdulmumini Usman, ya jagoranci dandazon jama'a zuwa yin sallar roƙon ruwa.

An yi sallar ne a filin idi, wanda babban limamin babban masallacin jihar Katsina, Imam Gambo Mustapha ya jagoranta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fadi dalilin yin doka domin rage ikon Sarkin Musulmi

An gudanar da Sallar rokon ruwa a jihar Katsina
Sarkin Katsina ya jagoranci jama'a zuwa wurin sallar rokon ruwa. Hoto: Muhammad Aminu Kabir
Asali: Facebook

An nemi jama'an Katsina su tsananta addu'o'i

Jaridar Punch ta rahoto cewa, an yi kira ga mazauna jihar da su tsananta addu'o'i domin samun amfanin gona mai kyau a wannan daminar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika, an yi kira ga al'ummar jihar da su roki Allah ya kawo sauki ga tsadar rayuwa, saukin kayan abinci da kuma kawo karshen matsalar tsaro a jihar.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka yi sallar mai suna Abdurrahman Bature, wanda ya zanta da Channels TV, ya jaddada tsananin buƙatar samun ruwan sama domin ceton amfanin gona.

Ya yi kira tare da tsawatarwa mazauna jihar da su ji tsoron Allah SWT a dukkanin lamuransu tare da kiyaye rayuwa mai nagarta.

"Laifuffuka na hana ruwan sama"

Bature ya kuma yi kira ga shugabannin da su yi mulkin gaskiya, inda yace matsalolin jihar da suka haɗa da ƙarancin ruwan sama da kashe-kashe suna da alaƙa da miyagun halayen jama'a.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wa matafiya wuta, sun yi awon gaba da mutane 20 a kan titi

Bature ya ce:

"Ko wannan kashe-kashen na babu gaira ba dalili na rayukan jama'a za su iya zama dalilin rashin ruwan sama har da miyagun ɗabi'u."

Wannan sallar rokon ruwan na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya ke fama da ƙaruwar farashin kayayyaki wanda ya haura zuwa kashi 40.

Gwamna ya ja jama'a zuwa rokon ruwa

A wani labari a can baya, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulqadir Mohammed ya jagoranci mutane a wurin sallar rokon ruwa.

Da yake jawabi bayan an idar da sallar, Gwamna Bala Mohammed ya ce jama'ar jihar sun dade su na sa ran ruwan sama amma shiru bai sauka ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel