Harin Bam a Borno: Majalisa Ta Bayyana Wurin da 'Yan Ta'adda Suka Fito

Harin Bam a Borno: Majalisa Ta Bayyana Wurin da 'Yan Ta'adda Suka Fito

  • Ana ci gaba da yin Allah wadai kan harin bam da wasu ƴan ƙunar baƙin wake suka kai a garin Gwoza na jihar Borno
  • Majalisar wakilai ta yi zargin cewa ƴan ta'addan da suka kai harin shigo da su aka yi daga wajen jihar domin aikata ta'addancin da suka yi
  • Bama-baman dai da aka tayar sun jawo asarar rayukan sama da mutane 30 yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar wakilai a ranar Talata ta yi zargin cewa shigowa aka yi da ƴan ƙunar baƙin wake mata da suka tayar da bam a jihar Borno.

Ƴan ƙunar bakin waken dai sun tayar da bama-baman ne a garin Gwoza a ranar Asabar insa suka kashe mutane da dama.

Kara karanta wannan

An cafke wasu daga cikin masu hannu a harin bam a Borno

Majalisa ta yi zargin an shigo da 'yan kunar bakin wake a Borno
Majalisa ta yi zargin shigo da 'yan ta'addan da suka tayar da bam a Borno aka yi Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Majalisa a kan tada bam a Borno?

Ƴan majalisar sun bayyana haka ne a bayan la'akari kan ƙudirin gaggawa da ɗan majalisa mai wakiltar Gwoza/Chibok/Damboa, Ahmed Jaha ya gabatar, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake Allah wadai da harin, Ahmed Jaha, ya bayyana cewa bincike ya nuna cewa ƴan ƙunar baƙin waken shigo da su aka yi.

Ya bayyana cewa ƴan ta'addan an ɗauko hayarsu ne, aka sauya musu tunani tare da shigo da su daga wajen jihar domin kai harin ƙunar baƙin waken a Gwoza, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Harin bam ɗin dai ya jawo sama da mutane 30 sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Akwai barazanar tsaro a Najeriya

Ɗan majalisar ya bayyana cewa tayar da bama-baman ya ƙara fito da barazanar ayyukan ta'addanci da ƙasar nan ke fuskanta.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun kwararo zuwa jihar Neja daga kasashen waje? An gano gaskiya

Ahmed Jaha ya gayawa majalisar cewa sama da mutane 180 ne suka samu munanan raunuka, inda suke karɓar magani a asibitoci daban-daban a jihar

Daga nan sai majalisar ta buƙaci jami'an tsaro da su ƙara zage damtse wajen hana sake aukuwar irin hakan a nan gaba.

An cafke ƴan ƙunar baƙin wake a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumomi sun bayyana cewa an samu nasarar cafke wasu mata guda biyu da ake zargin ƴan ƙunar baƙin wake ne a jihar Borno.

An cafke ƴan ƙunar bakin waken ne dangane da tayar da bama-bamai a ƙaramar hukumar Gwoza wanda ya jawo asarar rayukan mutane masu yawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel