Sanusi vs Aminu Ado: Kotu Ta Yi Zama, An Dauki Mataki Kan Dambarwar Sarautar Kano

Sanusi vs Aminu Ado: Kotu Ta Yi Zama, An Dauki Mataki Kan Dambarwar Sarautar Kano

  • Babbar Kotun jihar Kano ta dage ci gaba da sauraron shari'ar da ake yi kan rigimar sarautar jihar zuwa ranar Alhamis
  • Kotun ta dauki matakin ne bayan kwamishinan Shari'a da kakakin Majalisar jihar sun shigar da korafi kan lamarin
  • Masu karar sun bukaci kotun da dakatar da tubabbun sarakuna ci gaba da kiransu a matsayin jagororin yankunansu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Babbar Kotun jihar Kano da ke sauraron korafi kan rigimar sarautar jihar ta dauki mataki a yau Talata 2 ga watan Yulin 2024.

Kotun ta dage ci gaba da sauraron shari'ar sarautar har zuwa ranar Alhamis 4 ga watan Yulin 2024.

Kara karanta wannan

Sokoto: Halin da ake ciki bayan fara sauraron ra'ayin jama'a kan dokar masarautu

Kotu ta dage ci gaba da sauraron shari'ar sarautar Kano
Kotu ta dage ci da sauraron shari'ar sarautar Kano zuwa jibi Alhamis. Hoto: @HrhBayero/ Muhammad Sanusi II.
Asali: Twitter

Kano: Korafin da aka shigar gaban kotun

Kwamishinan shari'a a jihar Kano da Majalisar jihar da kakakinta su suka shigar da korafi a gaban kotun, Daily Nigerian ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu korafin sun shigar da karar domin bukatar kotun ta dakatar da Aminu Ado da sauran sarakuna hudu ci gaba da kiran kansu sarakuna.

Lauyan masu kara Ibrahim Isah-Wangida shi ya shigar da korafin a ranar 27 ga watan Mayun 2024, cewar Peoples Gazette.

Wadanda ake kara kan sarautar Kano

Wadanda ake karar sun hada da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da na Bichi, Nasiru Ado Bayero.

Sauran sun hada da Sarkin Karaye, Dakta Ibrahim Abubakar da Sarkin Rano, Alhaji Kabiru Muhammad da Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim Gaya.

Bukatar lauyan Aminu Ado a kotu

Lauyan Aminu Ado ya ki amincewa da bukatar lauyoyin masu kara inda ya bukaci dage sauraron karar domin ba shi damar martani kan duka korafe-korafen.

Kara karanta wannan

"Kul fa": Cibiyar shari'ar Musulunci ta yi gargadi mai tsauri kan taɓa kimar Sultan

Bayan sauraron duka bangarorin biyu, Mai Shari'a, Amina Adamu Aliyu ta dage ci gaba da shari'ar zuwa ranar 4 ga watan Yulin 2024.

Ana rokon a hana gwamnan Kano biza

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya yi martani kan bukatar wata kungiya na neman hana gwamnan Kano da mukarrabansa fasfo a Najeriya.

Sanatan ya ce bukatar hakan daga wata kungiya kawai saboda rikicin masarauta a jihar abin dariya ne.

Shehu Sani ya yi martanin ne bayan kungiyar ta bukaci dakatar da duk wani taimako da hadaka daga hukumomin kasashen duniya ga Abba Kabir.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel