Rikicin Siyasar APC Ya Dawo Sabo, Sanatan Zamfara Ya Farfado da Wani Tsagin Jam’iyyar

Rikicin Siyasar APC Ya Dawo Sabo, Sanatan Zamfara Ya Farfado da Wani Tsagin Jam’iyyar

  • A halin yanzu dai rikicin cikin gida ya sake kunno kai a cikin APC yayin da Sanata Marafa ya sanar da dawowar wani tsagin jam'iyyar
  • Tsohon sanatan na Zamfara ta tsakiya ya ce ya farfado da tsagin jam'iyyar ne saboda ya fahimci an cire shi daga sabgar APC a jihar
  • Sanata Marafa ya kuma yi cikakken bayani kan zargin da aka yi cewa tsagin jam'iyyar da ya jagoranta ne ya yi karar APC a zaben 2019

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kaduna - Jigon APC a jihar Zamfara, Sanata Kabiru Marafa ya sanar da dawowar shugabancin wani tsagin jam'iyyar yayin da rikicin cikin gida ya sake mamaye APC a jihar.

Kara karanta wannan

Nyesom Wike: Ministan Tinubu ya gigita 'yan Najeriya da rigar kusan Naira miliyan 3

Sanata Marafa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da daruruwan magoya bayansa da suka yi takanas daga Zamfara suka ziyarce shi a Kaduna.

Sanata Kabiru Marafa ya yi magana kan shugabancin APC a Zamfara
Sanata Marafa ya gana da magoya bayansa a kan shugabancin APC a Zamfara. Hoto: @SenKGMarafa
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsagi biyu ne ke gudanar da shugabancin APC a Zamfara tun bayan da rikici ya balle a jam'iyyar lokacin gwamnatin Yari da kuma Matawalle.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Marafa ya farfado da tsagin APC

Sanatan wanda ya wakilci Zamfara ta tsakiya a majalisar tarayya ya ce yanzu ya farfado da tsagin da yake jagoranta saboda an cire shi da magoya bayansa daga tarurrukan jam'iyyar na baya-bayan nan a jihar.

Ya amince cewa rikicin jam'iyyar ne ya kai ga faduwarta babban zaben jihar, in aka cire na shugaban kasa, lokacin da yake jagorantar kungiyar yakin zaben Tinubu/Shettima.

Marafa ya kai APC kotu a 2019?

Kara karanta wannan

An shiga jimamin mutuwar wata Farfesa cikin wani yanayi maras dadi a gidanta a Maiduguri

Amma da yake tsame kansa daga rikicin jihar, ya karyata masu jita-jitar cewa tsaginsa ne ya shigar da APC kara a kotu a shekarar 2019, in ji rahoton jaridar Guardian.

Sanata Marafa ya bayyana cewa jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta gudanar da zaben fidda gwani ba bisa ka'ida ba, kuma aka garzaya kotu domin bin kadin lamarin.

Zamfara: APC ta yi taron dinke baraka

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar APC reshen Zamfara a ƙarƙashin jagorancin Tukur Danfulani, ta fara shirin dinke barakar da take fama da ita.

Jam’iyyar ta APC ta yanke shawarar gudanar da taro na wata-wata da nufin hada kan dukkanin mambonta ta yadda za su zama tsintsiya madaurinki daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel