Rikicin siyasar Zamfara: Kana da damar ficewa daga APC - Marafa ya caccaki Yari

Rikicin siyasar Zamfara: Kana da damar ficewa daga APC - Marafa ya caccaki Yari

Dan takarar gwamnan jihar Zamfara kuma shugaban kwamitin harkokin man fetur na majalisar dattijai, Kabir Garba Marafa, ya ce kofa bude take ga gwamnan jihar Abdu'aziz Yari na jihar Zamfara, a duk lokacin da ya so ficewa daga jam'iyyar APC.

Marafa a cikin wata sanarwa wacce ya sanyawa hannu da kansa a Abuja, ya bukaci gwamnan ya bar APC saboda ganin cewa ya kammala cimma duk wasu munanan muradun siyasar sa a cikin jam'iyyar.

"A yanzu, kofa a bude ta ke gareshi. Na tabbata zai tsinci ayyukan da ya shuka a APC a cikin kowacce jam'iyya ya koma."

KARANTA WANNAN: Shehu Sani ya bani cin hancin N10m amma naki karba - Shugaban kwamitin zaben APC

Rikicin siyasar Zamfara: Kana da damar ficewa daga APC - Marafa ya caccaki Yari
Rikicin siyasar Zamfara: Kana da damar ficewa daga APC - Marafa ya caccaki Yari
Asali: Depositphotos

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan jihar ya yiwa kwamitin zaben da kwamitin gudanarwar jam'iyyar na kasa ya kafa, da kada su kuskura su sanya kafarsu a cikin jihar ma damar suna son tsira da lafiyarsu.

Marafa ya ce, "Duba da wannan barazana da gwamnan ya yi wa kwamitin, sai kuma ya bugi gaban kansa ya gudanar da zaben fidda gwani tare da bayyana sakamakon zaben da kansa. Ya karya dukkanin matakai da dokokin da hukumar INEC ta kafa."

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng