Sokoto: Halin da Ake Ciki Bayan Fara Sauraron Ra’ayin Jama’a Kan Dokar Masarautu

Sokoto: Halin da Ake Ciki Bayan Fara Sauraron Ra’ayin Jama’a Kan Dokar Masarautu

  • A yau Talata 2 ga watan Yulin 2024 za a fara jin ra'ayin jama'a kan sabuwar dokar kananan hukumomi da kuma masarautu a jihar Sokoto
  • Kwamitin Majalisar jihar ta mika kudirin dokar gyaran fuska game da masarautu wanda zai rage karfin ikon Sarkin Musulmi
  • Wannan mataki ya jawo ce-ce-ku-ce daga bangarori da dama na Najeriya inda ake ganin ana neman taba kimar Sarkin Musulmi ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Yayin da ake rigima kan dokar sauya tsarin masarautu a jihar Sokoto, za a fara sauraran ra'ayin jama'a kan lamarin.

A yau Talata 2 ga watan Yulin 2024 ne za a fara sauraran ra'ayin jama'a bayan kwamitin Majalisar jihar ya mika kudurin dokar gyaran fuska ga masarautu.

Kara karanta wannan

An shiga jimamin mutuwar wata Farfesa cikin wani yanayi maras dadi a gidanta a Maiduguri

Za a fara sauraran ra'ayin jama'a kan sabuwar dokar masarautun jihar Sokoto
A yau Talata 2 ga watan Yulin 2024 za a fara sauraran ra'ayin jama'a game da dokar masarautu a Sokoto. Hoto: @ahmedaliyuskt.
Asali: Twitter

Yadda dokar ta shafi masarautun jihar Sokoto

Sabuwar dokar ta shafi masautun jihar da kuma kanannan hukumomi wurin nadin hakimai wanda ke karkashin Majalisar Sarkin Musulmi, cewar BBC Hausa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin jihar tun farko ta ce ta dauki matakin ne domin gyara sashe na 76, kashi na biyu na dokar jihar ta shekarar 2008, Daily Trust ta tattaro.

Dokar ta tsallake karatu na farko da na biyu wacce za ta rage karfin ikon Sultan na nadin hakimai ba tare da sahalewar gwamna ba.

Kudirin ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya

Wannan mataki na gwanatin jihar ya jawo kace-nace yayin da 'yan kasar da dama suka ce matakin an yi ne a kokarin rage karfin ikon Sultan.

Har ila yau, Kungiyar kare hakkin Musulmai ta MURIC ta yi gargadi kan lamarin inda ta ce taba kimar Sultan neman taba Musulman Najeriya ne.

Kara karanta wannan

Kano: Dalilai 3 da za su hana Aminu Ado Bayero ƙwace sarauta daga hannun Sanusi II

Wasu daga cikin mambobin Majalisar jihar daga bangaren PDP mai adawa sun yi fatali da sabuwar dokar.

Mambobin suka ce dokar ba ta da wani fa'ida inda suka zargi kawai bita da kullin siyasa ne musabbabin dokar.

MURIC ta gargadi gwamnatin Sokoto

Kun ji cewa cibiyar dabbaka shari'ar Musulunci ta gargadi gwamnatin jihar Sokoto kan wasa da rawanin Sarkin Musulmi.

Cibiyar ta tura gargadin ne yayin da ake zargin Majalisar jihar ta tabbatar da wata doka da zata rage ikon Sultan kan nadin hakimai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel