Minista Ya Bayyana Hanyar da Za a Bi Wajen Inganta Harkar Ilimi a Najeriya

Minista Ya Bayyana Hanyar da Za a Bi Wajen Inganta Harkar Ilimi a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ɗaukar dawainiyar samar da ingantaccen ilimi a Najeriya yafi karfin gwamanti ita kadai
  • Saboda haka ta bukaci kungiyoyi da masu abin hannu su tallafawa gwamanti wajen samar da ilimi mai inganci a fadin Najeriya
  • Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya fadi haka yayin taron karrama Dakta Emeka Offor da matarsa Dakta Adaora Offor

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja- Ministan ilimi na kasa, Farfesa Tahir Mamman ya bukaci yan Najeriya su tallafi harkar ilimi a Najeriya.

Farfesa Tahir Mamman ya ce hakan ya zama dole matuƙar ana son cigaban ilimi a Najeriya domin nauyin ya yiwa gwamnati yawa.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Shehu Sani ya magantu da jin an nemi a hana Gwamna Abba fita kasar waje

Tahir Mamman
Minista ya bukaci a tallafawa harkar ilimi a Najeriya. Hoto: @ProfTahirMamman
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ministan ya bayyana haka ne yayin bikin karrama Dakta Emeka Offor da matarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kiran minista kan inganta ilimi

Ministan ilimi na kasa, Farfesa Tahir Mamman ya ce gwamnatin tarayya na kashe mukudan kudi kan ilimi amma idan dambu ya yi yawa bai jin mai.

Saboda haka ya bukaci kungiyoyi da masu hannu da shuni su kawo agaji domin tallafawa harakar ilimi yana mai cewa haka ne kawai zai samar da ingantaccen ilimi a Najeriya.

Emeka Offor ya tallafawa ilimi

Farfesa Tahir Mamman ya bukaci yan Najeriya su yi koyi da Dakta Emeka Offor wajen tallafawa ilimi a Najeriya.

Dakta Emeka ya ba jami'ar Najeriya watau UNN da jami'ar Nnamdi Azikiwe NAU kyautar N100m da N50m domin gudanar da ayyukan yadda ya kamata.

Gwamnati ta karrama Emeka Offor

Kara karanta wannan

Sarkin Damaturu ya fara yunkurin rage farashin abinci domin saukakawa talaka

A sanadiyar gudunmawar da yake ba ilimi ne gwamanti ta karrama Emeka Offor da digirin girmamawa.

Dakta Emeka Offor da matarsa Dakta Adaora Offor sun samu karramawa ne daga jami'o'in UNN da NAU, rahoton Peoples Gazette.

Za a binciki masu takardun bogi

A wani rahoton, kun ji cewa ministan ilimi Farfesa Tahir Mamman, ya ce gwamnatin tarayya za ta bankaɗo mutanen da ke da takardun bogi a Najeriya.

Tahir Mamman ya jaddada buƙatar kiyaye mutuncin ilimi tare da yin alƙwarin haɗa gwiwa da hukumomin da abin ya shafa domin dawo da martabar tsarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng