Tsohon Mijin Ministar Jonathan, Diezani Ya Maka Ta a Kotu Saboda Amfani da Sunansa
- Mijin tsohuwar ministar man fetur a gwamnatin Goodluck Jonathan, Diezani Alison Madueke ya shigar da ita kara gaban alkali
- Tsohon mijin mai suna Alison Amaechina Madueke ya buƙaci ministar ta daina amfani da sunansa saboda barazana da yake fuskanta
- Alison Amaechina Madueke ya bayyana abubuwan da yake buƙata tsohuwar matarsa ta yi tun da igiyar aurensu ta katse a yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Tsohon mijin ministar man fetur a gwamantin shugaba Goodluck Jonathan, Diezani Alison Madueke ya maka ta a gaban kotu.
Tsohon mijin ministar mai suna Alison Amaechina Madueke ya bukaci ta daina amfani da sunansa tun da aurensu ya riga ya mutu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Alison Amaechina Madueke ya bukaci ta daina amfani da sunansa ne saboda barazana da yake fuskanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buƙatar tsohon mijin Diezani Alison Madueke
Tsohon mijin ya bayyana cewa yana buƙatar Diezani ta dawo amfani da sunan da take amfani da shi (Agama) tun kafin su yi aure.
Bayan haka ya bukaci ta wallafa canza sunan a jaridun gida Najeriya da kasar Birtaniya domin al'umma su shaida, rahoton the Guardian.
Dalilin neman Diezani ta cire Alison AMadueke
Alison Amaechina Madueke ya bayyanawa babbar kotun jihar Legas inda ya shigar da kara cewa cigaba da amfani da sunansa barazana ne a gare shi.
Ya ce matuƙar ta cigaba da amfani da sunansa to ba zai kubuta ba tun da ana tuhumar ta da wawushe kudi da wasu laifuffuka a Najeriya da Birtaniya.
Yaushe auren Diezani Alison Madueke ya mutu?
Bincike ya nuna cewa auren Diezani da Alison ya mutu ne tun a shekarar 2021 bayan sun fara samun matsala a shekarar 2015.
Diezani ce ta shigar da kara a babbar kotun jihar Nasarawa domin kotun ta raba aure tsakaninta da Alison Amaechina Madueke.
Diezani Madukwe ta kai karar EFCC
A wani rahoton, kun ji cewa tsohuwar ministan man fetur, a gwamnatin Goodluck Jonathan, Diezani Alison-Madueke ta kai ƙarar hukumar EFCC gaban kotu.
A wancan lokaci Diezani Alison Madueke ta kuma haɗa da Antoni janar na gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, a cikin ƙarar da ta shigar gaban kotu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng