An Shiga Jimamin Mutuwar Wata Farfesa Cikin Wani Yanayi Maras Dadi a Gidanta a Maiduguri

An Shiga Jimamin Mutuwar Wata Farfesa Cikin Wani Yanayi Maras Dadi a Gidanta a Maiduguri

  • An shiga jimami bayan mutuwar wata Farfesa daga Jami'ar Maiduguri a cikin garejin motarta a ranar Lahadi
  • Marigayiyar mai suna Farfesa Ruth Wazis ta rasa ranta ne yayin da take ajiye motarta a cikin garejin gidanta
  • Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Yusuf Lawal shi ya tabbatar da haka inda ya ce an dauki gawarta zuwa asibiti

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Borno - Rundunar 'yan sanda a jihar Borno ta tabbatar da mutuwar wata Farfesar Jami'ar Maiduguri a wani irin yanayi.

Marigayiyar mai suna Farfesa Ruth Wazis wacce tsohuwar shugabar tsangayar harkokin kasuwanci ce ta rasu a cikin gidanta.

Farfsesa a Jami'ar Maiduguri ta rasa ranta a cikin gareji
Rundunar 'yan sanda a Borno ta tabbatar da mutuwar Farfesa Ruth Wazis a gidanta. Hoto: @BornoPoliceNG.
Asali: Twitter

Yadda Farfesa ta mutu a cikin gareji

Kara karanta wannan

Borno: Mutane sun mutu bayan wata ta kai harin bam kan masu zaman makoki

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Yusuf Lawal ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 30 ga watan Yunin 2024, cewar Zagazola Makama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce lamarin ya faru ne yayin da ta shiga garejin motarta domin ajiye, kwatsam sai motar ta zabura da gudu tare da buga ta kasa.

Hakan ya jawo faduwarta da kasa inda motar ta danne kirjinta wanda ya yi sanadin rasa ranta nan take, Daily Trust ta tattaro.

Ifila'in da ya faru ya jawo mata raunuka da dama a jikinta kafin daukarta zuwa asibiti domin daukar matakin gaba.

Mahaifiyar Sanata Sheriff ya rasu a Borno

Har ila yau, mun kawo labarin rasuwar Hajiya Aisha, mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Borno kuma jigo a jam'iyyar APC, Ali Modu Sheriff.

An ruwaito cewa Hajiya Aisha ta kwanta dama ne a ranar Lahadi 29 ga watan Yunin 2024 bayan doguwar jinya a wani asibitin Abuja.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: ASUU ta fadi matakin da ta dauka bayan ganawarta da gwamnatin tarayya

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya mika sakon ta'aziyya a madadin Shugaba Bola Tinubu.

Yar kunar bakin wake ta hallaka mutane

A wani labarin, kun ji cewa Akalla mutane shida ne suka rasa rayukansu bayan kunar bakin wake kan masu zaman makoki a jihar Borno.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 29 ga watan Yunin 2027 a karamar hukumar Gwoza da ke jihar da tsakar rana.

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Yusuf Lawal ya tabbtar da faruwar lamarin inda ya ce mace ce ta tayar da bam din.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.