Sarautar Kano: Shehu Sani Ya Magantu da Jin An Nemi a Hana Gwamna Abba Fita Kasar Waje

Sarautar Kano: Shehu Sani Ya Magantu da Jin An Nemi a Hana Gwamna Abba Fita Kasar Waje

  • Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan masarautu, wata kungiya ta bukaci hana Gwamna Abba Kabir da mukarrabansa fasfon zuwa ketare
  • Kungiyar ta zargi gwamnan da hannu dumu-dumu a rikicin masarautun jihar da kuma bijirewa umarnin kotu da ya kawo rigima kan sarauta
  • Sanata Shehu Sani ya yi martani kan bukatar kungiyar inda ya ce wannan abin dariya ne saboda rigimar masarautu a dauki wannan mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sanata Shehu Sani ya yi martani kan bukatar wata kungiya na neman hana gwamnan Kano da mukarrabansa fasfo a Najeriya.

Sanatan ya ce bukatar hakan daga wata kungiya kawai saboda rikicin masarauta a jihar abin dariya ne.

Kara karanta wannan

Kano: Dalilai 3 da za su hana Aminu Ado Bayero ƙwace sarauta daga hannun Sanusi II

Shehu Sani ya yi martani kan neman hana Abba Kabir fasfo
Shehu Sani ya caccaki kungiya da ke neman a hana Abba Kabir da mukarrabnsa fasfo. Hoto: Shehu Sani, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Shehu Sani ya soki kungiya kan Abba

Shehu Sani ya bayyana haka ne a jiya Litinin 1 ga watan Yulin 2024 a shafinsa na X bayan korafin wannan kungiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sani ya yi martanin ne bayan kungiyar ta bukaci dakatar da duk wani taimako da hadaka daga hukumomin kasashen duniya ga Abba Kabir.

Hakan ya biyo bayan rigimar masarautu a jihar da ake ci gaba da yi wanda ya ki ci ya ki cinyewa tun a watan Mayun 2024.

Kano: Kungiya ta bukaci hana Abba fasfo

Kungiyar mai suna The Save Kano Coalition ta bukaci Amurka ta kakaba dokar hana Abba Kabir da mukarrabansa fasfo saboda hannu a rigimar masarautu.

Ta zargi Abba Kabir da bijirewa umarnin kotu da kuma kawo rudani a jihar kan dambarwar masarautu da ke faruwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Gida Gida ta sake ware N600m domin ayyukan ci gaban Kano

"Neman hana fasfo ga Gwamna Abba Kabir da mukarrabansa saboda rigimar masarautu wannan abin dariya ne."

- Shehu Sani

Shehu Sani zai kalubalanci Wike

A wani labarin, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya sha alwashin kalubalantar Ministan Abuja, Nyesom Wike idan suka hadu.

Hakan ya biyo bayan kalaman Wike inda ya ke kalubalantar Shehu Sani da ya nuna ayyukan da ya yi lokacin da yake Sanatan Kaduna.

Sanatan ya ce ya gano ainihin dalili da kuma dabarar da ya sa Wike yake zama mai magana ta karshe duk lokacin da ake yin taro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel