Kano: KEDCO ya Yanke Wutar Lantarkin Jami'ar Aliko Dangote Saboda Taurin Bashi

Kano: KEDCO ya Yanke Wutar Lantarkin Jami'ar Aliko Dangote Saboda Taurin Bashi

  • Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya yanke wutar jami'ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote saboda taurin bashi
  • Kamfanin ya dauki matakin ne bayan mahukunta sun gaza biyan bashin N60m ga kamfanin, N20m kacal ya iya biya zuwa yanzu
  • Shugaban sashen kula da kula harkokin dalibai na jami’ar, Farfesa Abdulkadir Dambazau ya shaidawa manema labarai haka

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Hukumar jami'ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil ta shiga tsilla-tsilla bayan kamfanin rarraba hasken wuta, KEDCO ya yanke masu wuta.

Baki daya jami'ar, wanda mallakin gwamnatin jiha ce ta shiga duhu saboda gazawarta wajen biyan kudin wuta da ake bin ta bashi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jigawa ta fara shirin sayen jami'ar kuɗi, ta kafa kwamitoci 3

KEDCO
Taurin bashi ya sa KEDCO yanke wutar jami'ar Aliko Dangote Hoto: Daniel Balakov
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa mahukuntan jami'ar sun iya biyan N20m daga cikin N60m da KEDCO ke binta, inda kamfanin ya yanke shawarar yanke wutar kawai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karatu a duhu a jami'ar Dangote

Da yake sanar da halin da ake ciki ga manema labarai a Litinin nan, shugaban sashen kula da kula da harkokin dalibai na jami’ar, Farfesa Abdulkadir Dambazau, ya ce sun dogara ne kan wutar KEDCO.

Farfesa Dambazau ya jaddada cewa yanke wutar ya jefa baki daya jami'ar cikin damuwa ganin yadda ba su da hanyar samun haske, Daily Trust ta wallafa.

Ya ce jami’ar na bakin kokarinta wajen biyan kudin wuta daga Naira miliyan 16 zuwa 17, sai kamfanin KEDCO ya kara zuwa Naira miliyan 50, baya ga bashin da suke kokarin biya.

Yanzu haka jami'ar na tunanin ko da a rufe jami'ar, ko a bar dalibai su ci gaba da karatu da zaman makaranta a cikin tsananin duhu.

Kara karanta wannan

Kudin wuta: KEDCO ya maka kungiyar da yake zargi da jawo masa asarar biliyoyi a kotu

Kamfanin KEDCO zai jefa jama'a cikin duhu

A baya kun samu labarin yadda kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO zai fara yanke wutar wandanda suka hana shi kudinsa.

Shugaban sashen yada labarai na kamfanin, Ibrahim Shan Shawar ne ya bayyana haka, kuma abokan huldarsa da ke Kano, Katsina da Jigawa lamarin zai shafa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel