Kamfanin wutar KEDCO za ta jefa al’umomin Kano, Katsina da Jigawa cikin duhu

Kamfanin wutar KEDCO za ta jefa al’umomin Kano, Katsina da Jigawa cikin duhu

Kamfanin rarraba wutar lantarki ta KEDCO ta bayyana shirye shiryenta na fara yankan wuta n agama gari a jahohin Kano, Katsina da Jigawa sakamakon taurin bashi da tace jama’an garuruwan na da shi.

Shugaban sashin watsa labaru na KEDCO, Ibrahim Shan-Shawar ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta a garin Kano, inda yace zasu yanke wuta daga makarantu, kamfanoni, da gidajen rediyon da basa biyan kudin wuta.

KU KARANTA: Tiryan tiryan: Yadda yan bindiga suka sako daliban ABU 3 bayan sun karbi naira miliyan 5.5

“Mun yanke shawarar yankan wutan ne sakamakon hukumar dake dakon wutar lantarki a Najeriya, TCN, ta koka kan rashin sayen wuta da KEDCO bata yi, don haka zamu dauki wannan mataki don dawo da kudadenmu dake hannun jama’a, ta yadda muma zamu dinga biyan TCN kudinta cikakku.

“Daga watan Janairun 2019 zuwa watan Yulio kadai, KEDCO na bin jama’a bashin kudin wuta daya kai naira biliyan 10, hakan zai gurgunta kasuwanci ne kawai, musamman duba da cewa muma sayo wutar nan muke yi.

“Don haka da zarar mun fara yanka, zamu daina bayar da wuta a yankunan da matakin ya shafa.” Inji shi.

Daga karshe Shan-Shawai ya bayyanacewa hukumar KEDCO na fatan wannan mataki da za su dauka zai sanya jama’a su fara biyan kudin wuta cikin lokaci, tare da sauke nauyin bashin dake wuyansu.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar sake kwato kamfanin rarraba wutar lantarkin Najeriya, wanda yan Najeriya suka fi sani da tsohon sunansa ‘NEPA’ daga hannun yan kasuwa don ceto Najeriya daga matsanancin matsalar wuta da ake fama da shi.

Wannan mataki da gwamnati ke shirin dauka ya zo ne a daidai lokacin da za’a gudanar da cikakken nazari na karshe game da ayyukan kamfanonin rarraba wutar lantarki watau DISCOS, don tabbatar da ko suna aikinsu yadda ya kamata ko kuwa a’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel