Shugaban Majalisa Ya Fadi Abin da Za a Magance a Samu Zaman Lafiya da Cigaba a Afrika

Shugaban Majalisa Ya Fadi Abin da Za a Magance a Samu Zaman Lafiya da Cigaba a Afrika

  • Shugaban majalisar dokokin Najeriya, Abbas Tajudeen ya yi magana kan matsalolin da suka addabi yammacin Afirka a zamanin da muke ciki
  • Abbas Tajudeen ya bayyana abubuwan ne yayin zaman majalisar ƙasashen yammacin Afrika a yau Litinin a birnin tarayya Abuja
  • Har ila yau ya yi kira ga majalisar kan yin huɓɓasa wajen magance matsalolin domin samar da zaman lafiya da cigaba a yammacin Afrika

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kakakin majalisar dokokin Najeriya, Abbas Tajudeen ya yi magana kan tarin matsalolin da suka dabaibaye yammacin Afrika.

Kakakin majalisar ya yi magana ne a yau Litinin yayin taron majalisar yammacin Afrika (ECOWAS) a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci sun yi hannun riga da limami kan bijirewa basarake, sun ba da shawara

Abbas Tajudeen
Kakakin majalisa ya yi kira kan magance matsalolin Afrika ta yamma. Hoto: Abbas Tajudeen
Asali: Facebook

Jaridar the Nation ta ruwaito cewa Abbas Tajudeen ya yi kira na musamman ga majalisar nahiyar domin magance matsalolin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan matsalolin yammacin Afrika

Shugaban majalisar dokokin Najeriya, Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya bayyana cewa daga cikin manyan damuwar yammacin Afrika akwai 'yan bindiga.

Ya kara da cewa bayan ta'adin 'yan bindiga akwai safarar mutane, cin zarafin dan Adam, mummunan shugabanci da dumamar yanayi.

Yadda za a magance matsalolin Afrika

Abbas Tajudeen ya ce tarin matsalolin nauyi ne a kan majalisar da ya kamata ta yi nazari kan yadda za ta magance su.

Kakakin ya ce ya kamata majalisar ECOWAS ta kara ƙaimi da kwazo wajen ganin ta magance matsalolin domin samar da zaman lafiya da cigaba a yammacin Afrika.

Kokarin da majalisar ECOWAS ta yi

Duk da tarin matsalolin da ake fuskanta a yammacin Afrika, Tajudeen Abbas ya ce ba za a manta da kokarin da majalisar take ba, rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Ana kukan babu kuɗi, gwamnati na shirin ginawa ƴan majalisun tarayya katafaren asibiti

Ya bayyana cewa tun da aka kafa ECOWAS a shekarar 1975 take kokarin kare dimokuraɗiyya, hakkin dan Adam ba bin doka da oda.

Kasar Nijar za ta dawo ECOWAS

A wani rahoton, kun ji cewa dan majalisar wakilan kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta yamma, Ali Ndume ya ce kasashen da suka fita daga ECOWAS za su dawo.

Sanata Ali Ndume ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai bayan wani taron majalisar kungiyar da ya gudana a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng