Kishin Ƙishin Din Kara Kudin Fetur Ya Jawo Kulle Gidajen Mai, Jama’a Sun Shiga Tasko
- Al'ummar birnin Ibadan na jihar Oyo sun shiga babbar damuwa bayan kulle gidajen mai da yan kasuwa suka yi a jihar a safiyar yau Litinin
- Yanayin ya jefa masu motoci, babura da Keke NAPEP rashin samun wadataccen mai wanda hakan ya kawo karancin abubuwan hawa a birnin
- Al'ummar birnin sun bayyanawa manema labarai mummunan halin da suka shiga saboda rashin isassun abubuwan hawa bayan sun wayi gari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - Rahotanni da ke fitowa daga birnin Ibadan sun nuna cewa an samu karancin abubuwan hawa a safiyar yau.
Bincike ya tabbatar da cewa hakan ya faru ne sakamakon kulle gidajen mai da yan kasuwa suka yi a birnin Ibadan.
Jaridar Tribune ta ruwaito cewa kungiyar IPMAN ta yi taro a makon da ya wuce domin duba karin kudin mai a jihohin Oyo da Osun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rashin abubuwan hawa a Oyo
Wuraren da ake hawa mota a birnin Ibadan sun zamo kufai a safiyar yau inda aka hango al'umma sun yi carko-carko suna jiran motoci.
Haka zalika wuraren da ake samun babur da Keke NAPEP duk sun kasance da tarin jama'a amma babu abin hawa.
Ma'aikaciya ta rasa abin hawa
Wata ma'aikaciya mai suna Adenike Jayeola ta dade tana jiran abin hawa a bakin hanya amma abu ya gagara.
Adenike Jayeola ta ce babu alamar motar bas ko keke NAPEP da za ta hawu domin zuwa aiki a safiyar Litinin.
Ma'aikaci ya makara wajen zuwa aiki
Wani ma'aikaci mai suna Sanjo ya bayyana cewa ya shafe lokaci mai tsawo yana jiran abin hawa amma ya rasa, rahoton Leadership.
Mista Sanjo ya tabbatar da cewa rashin samun abin hawa a kan lokaci ya jawo masa yin lattin zuwa wajen aiki.
Garuruwan da ake tsadar mai a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa Jigar Jigawa ce ta fi ko ina tsadar man fetur a Najeriya inda ake sayar da lita daya a kan N937.50 kamar yadda rahoto ya nuna.
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta ce mafi saukin farashin da 'yan Najeriya ke sayen litar man fetur ya karu zuwa N769.62.
Asali: Legit.ng