Yadda Tirela Ta Wuntsila a Kano, Mutane Kusan 30 Sun Mutu
- Hukumar kiyaye haɗura ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano ta tabbatar da wani mummunan haɗarin mota da ya faru a kwaryar jihar
- Rahotanni sun nuna cewa mummunan haɗarin ya faru ne daura da babbar kasuwar Dangwaro a safiyar yau Litinin 1 ga watan Yuli
- Hukumar kiyaye hadura ta kasa ta yi gamsasshen bayani kan yadda haɗarin ya faru ta irin hasarar rayuka da dukiya da aka tafka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano ta tabbatar da faruwar haɗarin babbar mota a jihar.
Rahotanni sun yi nuni da cewa hadarin ya jawo hasarar rayuka masu yawa tare da jikkata mutane da dama.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hadarin ya faru ne a yau Litinin kusa da kasuwar Dangwaro a jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda hadarin ya faru a Kano
Hukumar kiyaye haɗura ta kasa ta bayyana cewa babbar mota kirar tirela dauke da mutane ce ta yi karo da wata mota.
Bayan motocin sun yi karo sai tirelar ba wantsila ta baya ta fadi a kasa tare da mutanen da ta dauko, rahoton Leadership.
Dalilin hadarin da ya faru a Kano
Kwamandan hukumar FRSC a Kano, Ibrahim Abdullahi ya tabbatarwa da cewa hadarin ya faru ne sakamakon gudun da ya wuce ƙima da motocin ke yi.
Ibrahim Abdullahi ya kara da cewa lodin da tirelar ke dauke da shi ya wuce ƙa'ida wanda hakan ya kara munin haɗarin.
Mutanen da suka mutu a haɗarin
Hukumar FRSC ta tabbatar da cewa mutane kimanin 25 suka rigamu gidan gaskiya a sanadiyyar haɗarin motar.
Sai kuma mutane kimanin 53 da suka samu munanan raunuka kuma suna karbar kulawa a asibitin Murtala.
Rahotanni sun nuna cewa tirelar ta loda kaya ne tare da mutane za ta tafi kudancin Najeriya daga Maiduguri.
Tirela ta kashe masallata a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa an shiga wani irin yanayi bayan wasu masallata sun rasa ransu suna tsaka da sallah a masallacin Juma'a bayan tirela ta hau kansu.
An tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a garin Imawa da ke karamar hukumar Kura a jihar Kano a ranar Juma'a 28 ga watan Yunin 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng