FRSC Ta Bayyana Yadda Hadarin Mota Ya Maida Bikin Sallah Zaman Makoki a Jihohi

FRSC Ta Bayyana Yadda Hadarin Mota Ya Maida Bikin Sallah Zaman Makoki a Jihohi

  • Hukuma mai kula da haɗura ta ƙasa (FRSC) ta fitar da rahoto kan yadda bikin sallah ya gudana a wasu jihohin kudancin Najeriya
  • Rahoton da hukumar ta fitar ya nuna an samu haduran mota da dama wanda ya jawo asarar rayuka da jikkata mutane da yawa
  • Har ila yau, hukumar ta tattara rahoton ne a jihohi uku inda ga fara gudanar da aikin bada kulawa tun ranar Jumu'ar da ga gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kudu - Hukuma mai kula da haɗura ta ƙasa (FRSC) ta bayyana yadda aka samu haɗuran mota yayin bikin sallah.

Rahoton da hukumar FRSC ta fitar ya nuna cewa kimanin mutane 128 ne haɗuran suka rista dasu a jihohi uku.

Kara karanta wannan

'Kar ka fara da bada hakuri': 'Yan kasa sun yi martani ga Tinubu, sun fadi mafita ga Najeriya

Hukumar FRSC
FRSC ta fitar da rahoto kan haduran da aka yi a Oyo, Ondo da Osun a bikin sallah. Hoto: Federal Road Safety Corps Nigeria.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa rahoton da FRSC ta fitar ya shafi wasu jihohin kudu maso yammacin Najeriya ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bikin sallah: jihohin da aka yi hadari

Hukumar FRSC ta fitar da rahoto ne a jihohin Osun, Oyo da Ondo da suke kudu maso yammacin Najeriya.

Har ila yau hukumar ta tabbatar da cewa ta fitar da rahoton ne kan haɗuran da suka faru cikin kwanaki ukun salla na farko.

Yadda haɗuran sallah suka kasance

FRSC ta tabbatar da cewa an samu haɗuran mota wanda suka ritsa da kimanin mutane 128 da motoci 21, rahoton Tribune.

Hukumar ta tabbatar da cewa mutane kimanin 13 sun rasu, 78 sun samu munanan raunuka yayin da aka ceto 41 ba tare da jin rauni ba.

Shirin FRSC yayin bikin sallah

Jami'in FRSC mai kula da jihohin Osun, Oyo da Ondo Laye Adegboyega ya ce hukumar ta samar da jami'anta a manyan hanyoyi 65 a yankin.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun hallaka ƴan bindiga sama da 100 ana shagalin Sallah a Arewa

Laye Adegboyega ya ce sun samar da jami'ai 3,018, motoci 57 da sauran kayan aiki domin kiyaye haɗura a yankin.

An yi hadarin mota a Ogun

A wani rahoton, kun ji cewa ana cikin bikin babbar sallah wani mummunan hadarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da jikkata wasu a jihar Ogun.

Kakakin hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) a jihar Ogun, Florence Okpe ta tabbatarwa manema labarai faruwar hadarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng