An Kwace Kwangilar Hanyar da ta Haɗa Arewa da Kudu Hannun Dantata da Wasu Kamfanoni

An Kwace Kwangilar Hanyar da ta Haɗa Arewa da Kudu Hannun Dantata da Wasu Kamfanoni

  • Gwamnatin Najeriya ta kwace kwangilar babbar hanyar da ta tashi daga jihar Kogi a Arewa zuwa jihar Edo a kudancin Najeriya
  • Ministan ayyuka na kasa, Nweze David Umahi ne ya bayyana lamarin ga manema labarai tare da faɗin dalilin kwace kwangilar daga kamfanonin
  • Tun a watan Disambar 2012 gwamnatin tarayya ta ba kamfanonin kwangilar domin biyunta hanyar amma har yanzu aiki ya gagara kammala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Ministan ayyuka na kasa, Nweze David Umahi ya sanar da dakatar da kwangilar hanyar data haɗa jihohin Kogi da Edo.

Gwamnatin tarayya ta ba kamfanoni uku kwangilar aikin fadada titin tun shekarar 2012 amma sun gagara karasa aikin.

Kara karanta wannan

Kwara: Hukumar kwastam ta tatso harajin N10bn a cikin watanni 5

Aikin titi
Gwamnatin tarayya ta kwace kwangila daga kamfanoni. Hoto: Alexandrumagurean
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hadimin ministan ayyuka, Barista Orji Uchenna ne ya fitar da sanarwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanonin da aka ba kwangilar titin

Bayanan da ma'aikatar ayyuka ta kasa ta fitar ya nuna cewa kamfanin ayyuka na Dantata and Sawoe Construction na cikin wadanda aka ba kwangilar.

Cikin kamfanonin da aka ba kwangilar har ila yau akwai kamfanin ayyuka na Mothercat Ltd da RCC Ltd, rahoton jaridar Punch.

Dalilin kwace kwangilar babban titin

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kwace kwangilar ne sakamakon tafiyar hawainiya da aikin ke yi tun da aka fara shi a shekarar 2012.

Ta kuma kara da cewa rashin tafiyar aikin yadda ya kamata na cigaba da kawo rashin jin dadi ga mutane da suke tafiya a kan hanyar.

Mataki na gaba da gwamnati ta dauka

Kara karanta wannan

Gwamna ya faɗi sunan wanda ya tayar da bam, ya alaƙanta shi da ministan Tinubu

Ministan ya ba injiniyoyin ma'aikatar umurnin gaggauta karbar dukkan bayanan aikin daga kamfanonin domin samun yadda za a cigaba.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin ba za ta yi wasa ba wajen dakatar da duk wanda aka ga yana tafiyar hawainiya da kwangila da aka ba shi.

Minista ya soki dan kwangila

A wani rahoton, kun ji cewa David Umahi bai ji dadin aikin da ya gani a titin Amanwozuzu-Uzoagba-Eziama-Orie-Amakohia ba.

Rahotanni sun nuna cewa Ministan ayyukan na Najeriya ya soki kamfanin Fig Fyne Construction Company da aka ba kwangilar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel