Tirela Ta Sake Kashe Bayin Allah a Kano, Babbar Motar da Ta Dauko Mutane 90 Tayi Hadari

Tirela Ta Sake Kashe Bayin Allah a Kano, Babbar Motar da Ta Dauko Mutane 90 Tayi Hadari

  • Wata babbar mota dauke da fasinjoji akalla 90 ta gamu da hadari bayan gudun wuce sa'a da direban tirelar ke yi har ya jawo asarar rayuka
  • Mutane akalla 25 ne aka tabbatar sun riga mu gidan gaskiya, yayin da wasu 53 suka samu raunuka daban-daban, amma 12 sun tsira
  • Hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa reshen jihar Kano ta tabbatar da afkuwar hadarin, inda ta danganta shi da gudun wuce sa'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Mutanen da ke kusa da Dangwaro a gadar saman Kano-Zaria sun shiga tashin hankali bayan hadarin babbar mota ya kashe mutane akalla 25.

Kara karanta wannan

Borno: Mutane sun mutu bayan wata ta kai harin bam kan masu zaman makoki

Babbar mota mai dauke da mutane kimanin 90 ce ta yi hadari saboda abin da hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa (FRSC) ta kira da gudun ganganci.

Kano map
Mutane 25 sun mutu a hadarin mota Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa tirelar ta auno a guje ne sai motar ta kwacewa direba, lamarin da ya jawo wasu 25 suka rasa rayukansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wasu sun ji raunuka a Kano," FRSC

Mutane da dama sun jikkata a hadarin da ya afku ranar Litinin a jihar Kano, inda mutane 53 suka samu mabambantan raunuka, kamar yadda Daily Post ta wallafa.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Abdullahi Labaran ya tabbatarwa Legit afkuwar hadarin da ya ce an samu ceto wasu mutum 12 babu ko kwarzane.

FRSC ta yi gargadi bayan hadarin Kano

Hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa, reshen jihar Kano ta gargadi matuka manyan ababen hawa su guji gudun wuce sa'a.

Kara karanta wannan

Gini ya rufta kan mutane 2 a Abuja, gwamnati ta dauki matakin gaggawa

Shugaban hukumar a jihar, Ibrahim Abdullahi ya kuma ja kunnen masu daukar dabbobi, kaya da motoci yayin tafiye-tafiye.

Ya ce irin wannan na jawo munanan hadurra da ke kawo asarar rayuka, yayin da wasu za su iya samun mugayen raunuka.

Kano: Mota ta bi ta kan masallata

A baya mun kawo labarin yadda wata babbar mota ta kutsa cikin masallata a jihar Kano tare da kashe mutane 14 nan take.

Masallatan dake sallar Juma'a a garin Imawa da ke karamar hukumar Kura na tsaka da sallah lokacin da motar ta kwace ta shiga cikinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.