Kwara: Hukumar Kwastam Ta Tatso Harajin N10bn a Cikin Watanni 5

Kwara: Hukumar Kwastam Ta Tatso Harajin N10bn a Cikin Watanni 5

  • Hukumar kwastam ta kasa ta bayyana nasarar tattarawa gwamnati haraji mai tarin yawa cikin watannin Janairu zuwa Mayu
  • An tattara kudin shiga da N10.27 a jihar Kwara, yayin da aka cafke wasu haramtattun kaya masu dimbin yawa da ake shigowa da su
  • Shugabar hukumar a jihar Kwara, Faith Ojeifo ta ce kayan da aka kama sun hada da buhunhunan shinkafa da jarkokin man fetur

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kwara- Hukumar kwastam ta kasa ta bayyana nasarar tattara kudin shiga ga gwamnatin Najeriya da yawansu ya kai N10bn a cikin watanni biyar.

An tattaro kudin harajin N10.027bn a jihar Kwara daga watan Janairu 2024, zuwa watan Mayu a cikin shekarar.

Kara karanta wannan

Kudin wuta: KEDCO ya maka kungiyar da yake zargi da jawo masa asarar biliyoyi a kotu

Hukumar Kwastam
Hukumar kwastam ta tara harajin N10bn daga Mayu zuwa Janairu Hotu:Nigeria Customs Service
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa shugabar hukumar kwastam a Kwara, Faith Ojeifo ce ta bayyana haka, tare da bayyana cewa an kama kayan miliyoyin Naira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan aka kwatanta da shekarar 2023, hukumar ta samu karuwar kudin harajin da ta tara a irin wannan lokaci da N2.88bn.

"Mun kama haramtattun kaya," Hukumar kwastam

Hukumar kwastam ta kasa reshen jihar kwara ta bayyana kama haramtattun kaya na kudinsu ya kai N35,416,140, kamar yadda Business Day ta wallafa.

Hukumar hukumar a jihar, Faith Ojeifo ce ta shaidawa manema labarai haka a jihar yayin da ta ke bayanin ayyukansu cikin watanni shida.

Misis Ojeifo ta lissafa kayan da aka kama, kuma sun hada da buhu 507 na shinkafa 'yar waje, gwanjon motoci, gwanjon tayoyoyin mota 1,055, jarkokin man fetur 164.

Hukumar kwastam ta raba tallafi

Kara karanta wannan

Ruwa ya cinye wasu dalibai a hanyarsu ta dawo wa daga jarrabawa a Kaduna

Hukumar kwastam reshen jihar Kwara ta raba tallafi ga mambobin kungiyar matan jami'an kwastam domin karfafa masu.

An raba masu kayan ne domin tallafa masu wajen dogaro da kai yayin da mazajensu ke wasu garuruwan suna wani aikin.

Kwastam: Yadda ake shigo da kwaya

A wani labarin, kun ji cewa hukumar kwastam ta kasa ta bayyana gano dabarun da ake amfani da su wajen shigo da kwayoyi cikin Najeriya.

Shugaban hukumar, Adewale Adeniyi ya dora laifin shigo da miyagun kwayoyin kan wasu jami'ansu marasa kishi, inda ya ce za a hukunta su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.