Gwamnan Kano, Abba Ya Dauki Matakin Yaki da Masu Safarar Miyagun Kwayoyi

Gwamnan Kano, Abba Ya Dauki Matakin Yaki da Masu Safarar Miyagun Kwayoyi

  • Gwamnantin Kano ta dauki mataki na dakile duk wasu hanyoyi da masu safarar kwayoyi ke bi wajen samun mafakar shari'a a jihar
  • Wannan na zuwa bayan Gwamna Abba Yusuf ya gano cewa dillalan kwaya na karbo izinin kotu wajen sakin kayansu da aka kwace
  • Gwamnan jihar ya kuma ba hukumar KAROTA umarni na yin duk mai yiwuwa wajen ganowa, kwacewa da kuma lalata miyagun kwayoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta waiwayi dillalan miyagun kwayoyi, musamman wadanda ke neman mafakar shari'a yayin da aka kwace haramtattun kayansu.

Gwamna Abba Yusuf ya yi mamakin irin karfin halin wasu dillalan kwayar, wadanda ke zuwa kotu su karbo takardar izinin a saki kayansu da aka kwace.

Kara karanta wannan

Ina aka kai maƙudan kuɗin da aka ƙwato daga ɓarayin ƙasa a mulkin Buhari?

Gwamna Abba Yusuf ya yi magana kan masu safarar kwayoyi
Gwamnan Kano, Abba Yusuf ya waiwayi masu safarar kwayoyi. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a shafinsa na X ya ce gwamnan ya dauki mataki kan hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Kotu na daurewa dillalan kwaya gindi

Dawakin Tofa ya ce gwamnan Kano ya samu labarin abin da ke faruwa ne lokacin da ya ziyarci hukumar KAROTA domin ganin halin da take ciki.

Gwamna Yusuf ya yi mamaki matuka da ya ji cewa masu safarar miyagun kwayoyi na karbo takardun izinin kotu domin a saki kwayoyinsu da aka hukumar ta kwace.

Ya kuma yi mamakin yadda wasu alkalan jihar ke ba masu aikata laifin irin wannan takarda, yana mai cewa hakan na kawo cikas ga yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi.

Abba ya dauki mataki kan lamarin kwaya

A nan take, gwamnan jihar ya ba Antoni Janar na jihar umarni na yadda za a dakile masu safarar miyagun kwayoyi daga samun mafakar shari'a a nan gaba.

Kara karanta wannan

Jerin tsofaffin kwamishinonin Legas da Tinubu ya ba manyan mukamai a gwamnatinsa

Ya kuma ce akwai bukatar saman da hadin kai tsakanin fannin shari'a da gwamnati domin ganin an dakile masifar da ke tattare da safarar miyagun kwayoyi.

Sanarwar ta kuma ce Abba ya ba hukumar KARATO umarni na yin duk mai yiwuwa wajen ganowa, kwacewa da kuma lalata miyagun kwayoyi a fadin jihar Kano.

Majalisa ta yi dokar safarar kwayoyi

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar dattawa ta amince da wani kudurin doka na yanke hukuncin kisa ga wadanda aka kama suna safarar miyagun kwayoyi.

Wannan kudurin ya samu goyon bayan mafi rinjayen sanatoci, yayin da dokar ke kokarin ganin an dakile sha da fataucin miyagun kwayoyi a fadin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel