Shehu Sani Ya Fadi Matakin da Zai Dauka Kan Wike Bayan Idan Suka Hadu Nan Gaba
- Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya yi martani kan wasu kalamai da ministan Abuja, Nyesom Ezonwo Wike ya yi masa
- Sanata Shehu Sani ya bayyana damar da yake jira domin ya rama abin da ya kira cin fuskar da ministan Abuja ya masa a yayin wani taro
- Ministan Abuja, Nyesom Wike ya kalubalanci tsohon Sanatan bayan ya yi maganganu kan yadda suka ceto dimokuraɗiyya a Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sanata Shehu Sani ya yi martani kan maganar da ministan Abuja Nyesom Wike ya fada a kansa yayin wani taro.
Ministan Abuja , Nyesom Wike ya kalubalanci Shehu Sani da ya nuna ayyukan cigaba da ya kawo a lokacin da yake Sanata.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sanata Shehu Sani ya fadi wajen da yake son rama abin da ministan ya masa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehu Sani: 'Na gano wayon Wike'
Sanata Shehu Sani ya ce a yanzu haka ya gano dabarar da Wike yake wajen zama mai magana na karshe a wuraren taro.
Shehu Sani ya ce Wike na amfani da wannar dabarar domin ya fadi abin da babu mai masa martani a wajen taro bayan ya kammala magana.
Matakin da Shehu Sani zai dauka
Shehu Sani ya bayyana cewa zai yi maganin Wike idan suka kara haduwa a wajen taro ta inda ba zai bar sa ya yi na karshe ba.
Sanatan ya kuma bayyana cewa sai sun hadu a wajen taro zai yiwa Wike maratani kan maganganun da ya fada a kansa.
Shehu Sani: 'Wike na cin albarkacin mu'
Har ila yau, Sanata Shehu Sani ya ce har yanzu Nyesom Wike albarkacin yaki da mulkin soja da suka yi yake ci a Najeriya.
Ya ce da ba su yi yaki da mulkin soja ba, da Wike bai samu damar rike mukaman gwamanti ba a rayuwarsa, rahoton Channels Television.
Shehu Sani ya gargadi Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya riƙa duba cancanta wajen naɗa muƙamai a gwamnatinsa.
Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya gargaɗi Shugaba Tinubu kan yin irin kuskuren magabacinsa, Muhammadu Buhari wanda ya bar ofis a shekarar bara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng