Jirgin Sojojin Saman Najeriya Ya Yi Hatsari, Dakaru Sun Hallara a Kauyen Kaduna

Jirgin Sojojin Saman Najeriya Ya Yi Hatsari, Dakaru Sun Hallara a Kauyen Kaduna

  • Jirgin saman rundunar sojin saman Najeriya ya yi hatsari a wani ƙauye da ke karkashin Igabi a jihar Kaduna
  • Cike da gwanancewa tare da kiyaye dokar saukar gaggawa, matuƙin jirgin ya sauka tare da tsira da ransa a hadarin
  • Mazauna yankin sun hanzarta kai ɗauki bayan jin ƙarar faduwar jirgin, daga bisani sojoji suka mamaye wurin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Wani jirgin sojin saman Najeriya ya tafka hatsari a sa'o'in farko na ranar Litinin a ƙauyen Tani dake ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Wani ganau ba jiyau ba, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa, ya ce lamarin ya faru ne wurin ƙarfe 5 na asuba, wanda ya haifar da tashin hankali ga mazauna yankin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka sace basarake da wasu bayin Allah a Arewa

Jirgin sojojin Najeriya yayi hatsari
Kaduna: Jirgin NAF yayi hatsari, matukin ya fita. Hoto: Nigeria Air Force
Asali: Facebook

Jigin sojojin Najeriya yayi hatsari

Daily Trust ta tattaro cewa, jirgin mai saukar ungulu, wanda ke sararin samamiya yana aiki ya fuskanci wata babbar matsala wanda ta kai ga hatsarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cike da sa'a, matuƙin jirgin yayi nasarar bin ladubban saukar gaggawa wanda hakan yasa ya tsira da ransa.

Tuni mazauna ƙauyen Tami suka garzaya wurin da hatsarin ya faru, inda suka bada taimakon gaggawa tare da nuna jin dadinsu saboda ba a yi rashin rai ko ɗaya ba.

Mazauna sun kai wa jirgin sojoji dauki

"Mun ji ƙarar faduwar wani abu, wanda ya sa muka garzaya wurin da lamarin ya faru.
Mun yi mamaki matuka tare da samun nutsuwa bayan da muka tarar matuƙin jirgin yana nan da ransa."

-Inji mazauna garin.

Sojoji sun dura wurin da jirgin ya sauka

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda da barayin man fetur

Tawagar jami'an sojojin sama sun hanzarta isa wurin tare da kewaye shi kuma sun fara binciken farko, jaridar Tribune Online ta ruwaito.

Sun kange wurin da hatsarin ya faru domin hana shigar waɗanda ba hukuma ba tare da tabbatar da kariyar mazauna ƙauyen.

Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, Rundunar Sojin Saman Najeriya, bata fitar da takarda a hukumance ba game da lamarin.

Jirgin sojojin sama ya gamu da hatsari

A wani labarin, mun ruwaito cewa jirgin sojojin saman Najeriya ya gamu da hatsari a wani wuri mai nisan kilomita 3.5 daga filin jirgin saman soji na Kaduna.

An ruwaito cewa jirgin ya samu hatsarin ne lokacin da yake dawowa daga wani atisaye. Air Marshal Hasan Abubakar, ya ba da umarnin a gudanar da bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel