Gwamnoni Sun Bayyana Yadda Jihohi Za Su Ruguje Idan Aka Yi Ƙarin Albashi

Gwamnoni Sun Bayyana Yadda Jihohi Za Su Ruguje Idan Aka Yi Ƙarin Albashi

  • A yayin da ake cigaba da dambarwar karin mafi ƙarancin albashi tsakanin yan kwadago da gwamnati, gwamnoni sun yi magana
  • Gwamnonin jihohi sun nuna damuwa kan yadda gwamnatin tarayya ke kokarin mayar da mafi ƙarancin albashi zuwa N62,000 a Najeriya
  • Kungiyar gwamnonin Najeriya ta fitar da sanarwa kan yadda jihohin da dama za su durkushe idan aka ƙara albashin ya yi yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - An cigaba da samun sabani tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago kan maganar ƙarin albashi.

A lokacin da ake tsammanin shugaba Bola Tinubu zai bayyana mafi ƙarancin albashi, gwamnonin jihohi sun yi magana.

Kara karanta wannan

Ina aka kai maƙudan kuɗin da aka ƙwato daga ɓarayin ƙasa a mulkin Buhari?

Gwamnonin jihohi
Gwamnoni sun koka kan karin albashi. Abdul No Shaking
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnoni sun nuna rashin gamsuwa kan yadda ake kokarin mayar da mafi ƙarancin albashi zuwa N62,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsalar karin albashi zuwa N62,000

Gwamnonin jihohi sun bayyana cewa idan aka kara albashi zuwa N62,000. za su shiga damuwa sosai.

Kungiyar gwamnonin ta tabbatar da cewa hakan zai sanya su kara albashi da kashi 100% idan aka lura da cewa suna biyan N30,000 ne a yanzu.

Karin albashi: Abin da zai durkusa jihohi

Gwamnonin Najeriya sun bayyana cewa idan aka yi karin albashin zuwa N62,000 jihohi kadan ne za su iya saura da kudi a asusunsu, kamar yadda kungiyar ta wallafa a shafinta.

Idan kuma jihohi suka rasa kuɗi bayan biyan albashi to dukkan ayyukan za su tsaya daga nan sai rushewar gwamanti.

Wani mataki NLC za ta dauka?

A halin yanzu dai an zuba ido kan abin da kungiyar kwadago za ta fada bayan da gwamnonin suka fitar da wannar sanarwa.

Kara karanta wannan

IPMAN ta yi zama domin rage kudin litar mai, an bayyana sabon farashin da take bukata

Dama dai al'umma suna sauraron irin matakin da NLC za ta dauka domin ganin gwamnoni sun biya mafi ƙarancin albashi da gwamnatin tarayya za ta ayyana.

Shehu Sani ya ceci Obasanjo a kurkuku

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda suka yi zaman gidan yari cikin tsanani tare da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo

Shehu Sani ya bayyana yadda manyan barayi suka nufi yiwa tsohon shugaban kasar duka a gidan yarin amma ya ba shi kariya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng