Jihohin Arewa 3 Da Aka Samu Sabani Tsakanin Sababbin Gwamnoni da Sarakunan Gargajiya

Jihohin Arewa 3 Da Aka Samu Sabani Tsakanin Sababbin Gwamnoni da Sarakunan Gargajiya

  • Jihohin Arewa maso Yamma na fama da matsaloli da dama, daga cikin wanda ke daukar hankali a yanzu shi ne na taba muhibbar masarautu.
  • Zuwa yanzu, batun masarautuar Kano da na Sokoto na gaban kotu, ta nemi kowa ya tsaya a matsayarsa har sai an yi hukunci na gaba
  • Yayin da a jihar Katsina, gwamnati ta ce bahasi kawai ta ke nema da dalilan da zai sa hakima su ki fitowa hawan sallah ba tare da sanar da ita ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihohi uku a Arewacin kasar nan da su ka hada da Kano, Katsina da Sokoto na fama da matsalar sarauta, inda gwamnonin jihar ke nuna ikonsu.

Kara karanta wannan

Duk da gargadin Abba, an kafa tuta a fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero

Ga jerin jihohin da halin da masarautunsu ke ciki a yanzu;

Arewa
Jihohin Kano, Sokoto da Sokoto na fama da rikicin masarauta Hoto: Abba Kabir Yusuf/Dr. Umaru Dikko Radda/Ahmed Aliyu Sokoto TV
Asali: UGC

Gwamnonin da ke rigima da Sarakuna a Arewa

1. Jihar Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin sarauta da ake fama da shi a Kano ya kai wani mataki da ya samar da sarakuna biyu - Sarkin da aka tube amma ya ki amincewa da hakan, da Sarkin da aka nada amma wasu dalilai sun hana shi sakat.

Za a iya cewa rikicin masarautar Kano na yanzu ya samo asali tun a shekarar 2015 bayan rasuwar Sarki Ado Bayero a shekarar 2014.

A wancan lokaci, gwamnatin Kano karkashin Rabi'u Musa Kwankwaso ta nada Malam Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarki, kamar yadda Channels Television ta wallafa.

Kura ta lafa bayan nadin sarkin Kano

Bayan 'yar hatsaniya da aka samu, musamman daga masu goyon bayan nada daya daga 'ya'yan marigayi sarki Ado Bayero, kura ta lafa har sai shekarar 2020.

Kara karanta wannan

Jihohi 3 da ke zargin gwamnatin tarayya da yi masu katsalandan

A safiyar Litinin din 9 Maris, 2020 ne gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta sanar da tsige sarki Muhammadu Sanusi II, sannan ta yi gaggawar maye gurbinsa da Aminu Ado Bayero.

Daga baya gwamnatin ta kori Muhammadu Sanusi II daga Kano zuwa Loko da ke jihar Nasarawa, inda daga baya ya koma jihar Legas ya ci gaba da sabgoginsa.

Rikicin masarautu ya dawo sabo

A halin da ake ciki, gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta dawo da Sarki Sanusi karagarsa, tare da rushe masarautun da Abdullahi Umar Ganduje ya kawo.

Sai dai ba kamar yadda Sarki Sanusi II ya bar zancen ba a wancan lokaci, Sarki Aminu Ado Bayero har yanzu ya na Kano a matsayin sarki yayin da ake ta ka-ce-na-ce a kotu.

2. Jihar Sokoto

Duniya ta fara sanin halin da jihar Sokoto ke ciki sosai ne bayan kungiyar fafutukar kare hakkin musulmi (MURIC) ta zargi gwamnati da kokarin cire sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta ware N1bn domin muhimman ayyuka a bangaren lafiya

A wane hali ake ciki a Sokoto?

1. Kotu ta hana tsige wasu hakimai, amma gwamnati ta ce sun tsigu

2. Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ja kunnen gwamnati kan yunkurin tsige sarkin musulmi

3. Kungiyar MURIC ta ce har yanzu ana kokarin tsige sarkin musulmi, Sa'ad Abubakar II, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

3. Jihar Katsina

Zuwa yanzu bayun jihar Katsina na kama da za a yi ko ba za a yi ba, domin gwamnatin jihar ta dage kan cewa kawai bayani ta nema, kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa.

Tun a yammacin Lahadi labari ya bulla cewa gwamnatin ta rubuta wasika ga masarautar Katsina ta na neman bayanai kan wasu hakimai da su ka ki zuwa hawan sallah.

Kotu ta yi hukunci kan rikicin masarauta

A wani labarin kun ji cewa bbbar kotu da ke zamanta a Kano ta yanke hukunci kan rikicin masarautar Kano da ake tantamar wanene sarki.

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Bayero: Manazarci ya hango makomar sarautar Kano bayan hukuncin kotu

Kotun ta jingine dokar da ta maido sarki Muhammadu Sanusi II kan karagarsa, amma lamarin bai shafi rushe sarakuna ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.