Malaman Musulunci Sun Yi Hannun Riga da Limami Kan Bijirewa Basarake, Sun Ba da Shawara

Malaman Musulunci Sun Yi Hannun Riga da Limami Kan Bijirewa Basarake, Sun Ba da Shawara

  • Yayin da ake rikici tsakani basarake da babban limamin gari, gamayyar malaman Musulunci sun tsoma baki
  • Kungiyar malaman Musulunci a Ogbomoso da ke jihar Oyo ta kalubalanci Sheikh Taliat Yunus kan bijirewa umarnin Oba Afolabi Ghandi
  • Hakan ya biyo sabanin da limamin ya samu da basaraken kan zuwa aikin hajji ba tare da izninsa ba wanda ya jawo rudani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Gamayyar limamai da malaman Musulunci a Ogbomoso sun soki limamin masallacin garin kan rigimarsa da Oba Afolabi Ghandi.

Malaman sun zargi Sheikh Taliat Yunus da rashin biyayya ga basaraken kan halartar aikin hajji a kasar Saudiyya babu izininsa.

Kara karanta wannan

An sanya ranar da gwamna zai mika sandan girma ga sabon sarkin Ibadan

Malaman Musulunci sun tsoma baki a rigimar limamin gari da basarake
Malaman Musulunci sun caccaki limamin Ogbomoso kan bijirewa umarnin basarake, Oba Afolabi Ghandi. Hoto: Afolabi Ghandi, Taliat Yunus.
Asali: Facebook

Oyo: Malaman Musulunci sun caccaki limamin Ogbomoso

Kungiyar ta bayyana haka ne a jiya Asabar 29 ga watan Yunin 2024 yayin ganawa da manema labarai a Ogbomoso, Tribune ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bayyana abin da limamin ya yi da cewa ba rashin daraja Oba na Ogbomoso kadai ya yi ba har ma da sarautar gargajiya a jihar.

Malaman sun kara da cewa a Musulmai a garin ba za su taba barin wani ya taba martabar basaraken ba, cewar Sahara Reporters.

Oyo: Malaman sun bukaci mutunta basaraken Ogbomoso

A martaninsa, Balogun Musulumi, Alhaji Bello Ayobami ya ce Musulmai ba za su taba bari wasu su jawo rashin jituwa a Ogbomoso da ke jihar Oyo ba.

Ayobami ya ce tun shekarar 1818 nadawa da sauke limamin Ogbomoso na hannun basaraken garin tun asali.

Kara karanta wannan

Kungiyar musulmi ta yi ƙarar sarkin Ogbomoso, kotu ta haramta tsige limamin Juma'a

Ya ce shekaru da dama ba a taba samun sabani a Ogbomoso ba duk da bambance-bambancen addinai a garin.

Har ila yau, ya ce Oba Afolabi ya na da ikon naɗa duk limamin daya ga dama daga kowane gidan Musulmai a Ogbomoso.

Basarake ya dauki mataki kan babban limami

Kun ji cewa Oba na Ogbomoso da ke jihar Oyo, Afolabi Ghandi ya kalubalanci babban limamin garin Sheikh Taliat Yunus kan bijirewa umarninsa.

Basaraken ya caccaki shehin malamin kan zuwa aikin hajji a Saudiyya ba tare da sanar da shi ba kamar yadda aka yi yarjejeniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel