Mutane 3 Sun Mutu, Gidaje 50 Sun Lalace Yayin da Ruwan Sama Ya Yi Barna a Jihar Arewa

Mutane 3 Sun Mutu, Gidaje 50 Sun Lalace Yayin da Ruwan Sama Ya Yi Barna a Jihar Arewa

  • Rahotanni sun nuna cewa akalla mutane uku ciki har da yaro dan shekara bakwai sun mutu a karamar hukumar Nangere, jihar Yobe
  • Mutuwar mutanen ta faru ne sakamakon ruwan sama da ya sauka kamar da bakin kwarya a yankin, wanda ya yi silar lalacewar gidaje
  • Da yake mayar da martani kan iftila'in, shugaban hukumar YOSEMA, Dakta Goje Muhammad ya jajanta wa wadanda abin ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Yobe - Akalla mutane uku ne suka mutu yayin da 7 suka samu raunuka bayan da wani gini ya rufta kansu sakamakon ruwan sama a karamar hukumar Nangere da ke jihar Yobe.

An tattaro cewa ruwan saman da ya sauka kamar da bakin kwarya ya lalata gidaje sama da 50, lamarin da ya sa iyalai da dama suka rasa matsuguni.

Kara karanta wannan

Borno: Mutane sun mutu bayan wata ta kai harin bam kan masu zaman makoki

Hukumar YOSEMA ta yi magana kan ruwan sama a Yobe
Ruwan sama ya yi ajalin mutane uku da lalata gidaje a Yobe. Hoto: KOLA SULAIMON
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a Tsohon Gari da ke hedikwatar karamar hukumar Nangere a karshen makon nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ruwan sama ya yi barna a jihar Yobe

Shuwa Adamu wani mazaunin al’ummar ya shaida wa manema labarai cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska mai karfi ne ya yi gyara.

A cewar Shuwa Adamu:

"Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a da misalin karfe 9 na safe lokacin da mazauna garin da dama ke shirin fara kasuwancinsu na yau da kullum.
“Akalla shaguna da gidaje 50 ne suka lalace sannan kuma an rasa ran wani yaro dan shekara bakwai.
"Jami'an hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Yobe sun tantance irin barnar da aka yi yayin da suka gudanar da bincike."

Ruwan sama ya yi ajalin mutane da dama

Kara karanta wannan

Kano: Ana fargabar mutane sun mutu yayin da gini ya rufta kansu ana ruwan sama

Wata mazauniyar yankin da ta bayyana sunanta da Halima ta ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska mai karfi ya yi sanadiyyar kashe mutane uku tare da lalata dukiyoyi.

"Sama da gidaje 50 ne suka lalace yayin da mutane 3 ciki har da yaro dan shekara bakwai suka mutu a cikin wani gini da ya rufta kan su.
"Wadanda suka rasa muhallansu a halin yanzu sun nemi mafaka a gidajen 'yan uwansu, a wurare daban daban."

- Inji Halima.

Gwamnatin Yobe ta yi martani kan iftila'in

Da yake mayar da martani kan iftila'in, babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Yobe (YOSEMA) Dakta Goje Muhammad ya jajanta wa wadanda abin ya shafa.

Ya ce hukumar ta dauki nauyin biyan kudaden jinyar duk wadanda suka jikkata a babban asibitin Nangere, inda ya ce zuwa yanzu wadanda suka jikkata an sallame su.

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane uku

Kara karanta wannan

Mummunan gobarar dare ta tashi a kasuwar Abuja, an gargadi mazauna yankin Karu

A wani labarin, mun ruwaito cewa ambaliyar ruwa a garin Dakingari da ke jihar Kebbi ta yi sanadin mutuwar mutane uku da lalata gidaje da dama.

Shugaban ƙaramar hukumar Sulu, Alhaji Muhammad Lawal Suru ne ya bayyana hakan yayin da ya nemi jama'a da su guji yin gine gine a hanyoyin ruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel