Hotuna: Anbaliyan ruwa yayi barna a jihar Yobe
-Sama da mutane 100 sun rasa gidajen su ta sanadiyar ambaliyar ruwan
-Maikatan hukumar agaji na gaggawa SEMA sun ziyarci garin
- Gwamana Ibrahim Gaidam ya ba da umarni taimakawa wadanda ambaliyan ya shafa
Sama da mutane 100 a jajimaji, dake karamar hukumar Karasuwa a jihar Yobe, sun rasa gidajen su ta dalilin ambaliyan ruwa. Yan jarida SUN ba da rahoton cewa “ruwan da akayi a safiyar Asabar da ya dauki sa’o’I da yawa shi ya haifar da matsalar ambaliyan ruwan.
“Sanadiyar haka mutane da yawa sun fice daga gidajen su, kuma sunyi hasaran dukiyoyi da amfanin gonakin su,” Inj Alhaji Ubaliyo.
Shugaban karamar hukumanAlhaji Ubaliyo Gambo, ya gaya ma manema Labarai cewa maikatan hukumar agajin gaggawa na jihar(SEMA) sun ziyarci wajen dan dan kawo agaji.
KU KARANTA:Yan bindiga sun kashe mataimakin Gwamna Samuel Ortom
Seketare dindindin na ma’aikatan SEMA alhaji Musa Jigawa yace“Gwaman jihar Yobe Ibrahim Gaidam ya umarce su da su duba iya barnan da ambaliyan yayi wadanda abun ya shafa dan kawo musu agaji.” Ya lura da cewa wajen yana yawan samu matsalar ambaliyar ruwa, ya kuma ba da shawarar yin hanyoyin ruwa ko kuma mutanen dake zama a garin su tashi zuwa wani wuri.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng