Ruwa zai yi gyara: Masana sun ce za a iya barkewa da ambaliya a Jihohi 34 na tsawon kwana 3

Ruwa zai yi gyara: Masana sun ce za a iya barkewa da ambaliya a Jihohi 34 na tsawon kwana 3

  • Hukumar NIMET ta ce za ayi fama da ambaliyar ruwa daga jiya zuwa gobe
  • Hasashen NIMET ya nuna ruwa zai iya barkewa a ranar Talata har Alhamis
  • An bada jerin jihohin da ake tunanin za su iya gamu wa da wannan matsalar

Abuja - Hukumar NIMET mai kula da yanayin gari ta yi gargadi cewa akwai yiwuwar a samu ambaliya a wasu jihohi 34 da ke Najeriya kwanan nan.

Watakila ruwa zai yi gyara

Da ta ke magana a ranar Talata, 23 ga watan Agusta, 2021, hukumar ta NIMET ta ce hakan na iya faru wa nan da kwana uku a cikin makon da ake ciki.

Matsakaita da ruwa mai nauyin da ake yi a halin yanzu za su iya kai ga samun ambaliya mai mugun karfi daga ranar Talata, zuwa Laraba, har Alhamis.

Kara karanta wannan

Farfesa Aminu Dorayi: Bakanon da ya tuko motarsa daga Landan har zuwa Kano

The Nation ta ce NIMET ta yi wannan bayani a wani jawabi da ta fitar ranar Talata ta bakin shugabanta na sashen hulda da jama’a, Muntari Ibrahim.

Irin wannan ambaliya da ake samu a tsakiyar damina ya fi tasiri ne a yankunan da ke kan gangare.

Ina da ina za a samu ambaliyar?

Kamar yadda hukumar ta bayyana, ambaliyar za ta yi tasiri a jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina, Kaduna, Kano, Jigawa, Bauchi, Gombe, Yobe, da Kebbi.

Ruwa ya yi gyara
Ambaliyar ruwa a kasar waje Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Ragowar jihohin sun hada da Filato, Adamawa, Taraba, da Kwara, sai kuma birnin tarayya Abuja.

Lamarin zai iya shafan Oyo, Legas, Ondo, Ogun, Edo, Delta, Bayelsa, Kuros Riba, Akwa Ibom, Benuwai, Enugu, Ebonyi, Imo, Anambra, Abia da Ribas.

NIMET ta ce za a iya ganin ruwa ya barke a tituna, gonaki, muhalli da gadoji da ke kan hanya, wanda hakan zai iya jawo hadari, motoci su zame a titi.

Kara karanta wannan

Magama-Saminaka: An yi kira ga Gwamnatoci su gyara titin da zai sa a daina kashe Matafiya a Jos

Rahoton yace hukumar ta gargadi mutane su dauki matakan da suka dace domin kare kansu daga aukuwar wannan musiba da za ta iya jawo asara.

Hukumar NIMET ta yi kira ga ‘yan Najeriya cewa ka da suyi wasa da hasashen da aka yi domin duk abin da aka fada a karshen watan Yuli, sai da ya tabbata.

'Yan bindiga a NDA

Bayanai suna zuwa game da yadda 'yan bindiga suka shiga NDA, an ji barci ne ya ci karfin Sojojin da aka tanada a dakin CCTV, har 'yan bindiga suka yi ta’adi.

Masu lura da CCTV suna barci a lokacin da aka sadada cikin makarantar Sojojin da ke garin Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel