Shehu Sani Ya Fadi Abin da Shugabannin Arewa Ya Kamata Su Mayar da Hankali a Kai

Shehu Sani Ya Fadi Abin da Shugabannin Arewa Ya Kamata Su Mayar da Hankali a Kai

  • Sanata Shehu Sani ya buƙaci shugabannin Arewa da su mayar da hankali kan harkar ilmi a yankin saboda muhimmancin da yake da shi
  • Tsohon sanatan mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa ya koka kan yadda harkar ilmi ta taɓarɓare musamman a Arewacin Najeriya
  • Ya nuna cewa akwai buƙatar shugabanni su tashi tsaye domin dawo da martabar ilmi a yankin saboda a yanzu ya zama koma baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani ya yi kira ga shugabannin Arewa da su ba ilmi muhimmancin gaske.

Sanata Shehu Sani ya buƙace su da su ɗauki ilimi da gaske domin kaucewa rugujewar makarantun gwamnati.

Kara karanta wannan

Mutumin da ya yi aiki da El-Rufai ya yi maganar wawurar N423bn a tsohuwar gwamnati

Shehu Sani ya shawarci shugabannin Arewa
Shehu Sani ya ba shugabannin Arewa shawara Hoto: Shehu Sani
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta ce ya yi kiran ne a wajen bikin cika shekaru 40 na kwalejin kimiyya ta gwamnati da ke Kagara a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja, a ranar Asabar, wacce ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na shekarar 1984 ta shirya a Minna, jihar Neja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Shehu Sani ya ce kan ilmi a Arewa?

Shehu Sani ya ce a da makarantun gwamnati sun kasance mafi kyawun makarantu wajen samun ilimi domin suna da malamai daga ciki da wajen Najeriya, rahoton jaridar The Cable ya tabbatar.

"Abin takaici ne yadda a yau wasu daga cikin makarantun gwamnati da suka samar da nagartattun mutane a tarihin ƙasar nan suka zama koma bayan yadda suke a baya."
"A zamaninmu a makarantu, muna da malamai daga Pakistan, India, Canada da Masar, a cikinmu yanzu akwai farfesoshi, likitoci, injiniyoyi, sanatoci, janar-janar na soja da sauransu."

Kara karanta wannan

Tsohon sanata ya bayyana bangaren da Tinubu ya yiwa Buhari fintinkau

"Abin takaici ne yadda makarantun gwamnati suka zama a yau, musamman a Arewa, dole ne Arewa ta ɗauki ilimi da muhimmanci, domin ta zama koma baya wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta."

- Sanata Shehu Sani

Tsohon Sanatan ya koka kan yadda ayyukan ƴan bindiga da ƴan ta’adda suke kawo tangarɗa ga ilmi a Arewacin Najeriya.

Shehu Sani ya magantu kan rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Shehu Sani, ya yi magana kan ƙalubalen rashin tsaron da Arewacin Najeriya yake fuskanta a lokacin Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon sanatan ya yi iƙirarin cewa ƙalubalen tsaron da Arewacin Najeriya ya fuskanta a lokacin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya fi na Shugaba Bola Tinubu muni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng