An Sanya Ranar da Gwamna Zai Mika Sandan Girma Ga Sabon Sarkin Ibadan

An Sanya Ranar da Gwamna Zai Mika Sandan Girma Ga Sabon Sarkin Ibadan

  • A ranar 12 ga watan Yulin 2024 gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde zai mika sandar girma ga sabon sarkin Ibadan, Oba Owolabi
  • Kwamishinan yada labarai na jihar Oyo, Prince Dotun Oyelade wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar
  • Tun da fari, Gwamna Makinde ya amince da naɗin Oba Owolabi biyo bayan shawarin da ya karɓa daga majalisar masarautar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da nadin sarauta tare da gabatar da sandar girma ga sabon sarkin kasar Ibadan, Oba Owolabi Olakunlehin.

An shirya gudanar da bikin mika sandar girman ne a ranar Juma'a 12 ga Yuli, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta mayar da martani kan ɗaga tuta a fadar da Aminu Ado ke zaune

Gwamna ya tsayar da ranar nadin sarautar sarkin Ibadan
Gwamnatin Oyo ta ware ranar mika sandar girma ga sabon sarkin Ibadan. Hoto: @seyiamakinde
Asali: Facebook

Kwamishinan yada labarai na jihar Oyo, Prince Dotun Oyelade wanda ya bayyana hakan kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna zai ba sabon sarki sandar girma

Prince Dotun ya bayyana cewa:

"Ya zama wajibi ga mutanenmu su koyi haƙuri kuma su kara mika yardarsu ga gwamnatin da ba ta taba gaza masu ba a cikin shekaru biyar."

Jaridar Tribune ta ruwaito Prince Dotun ya ce zage-zage da munanan kalamai ba su kawar da Makinde daga tafarkin adalci da gaskiya wajen shugabantar jama'ar Oyo ba.

Ya shawarci al’ummar Jihar Oyo da Ibadan da su kasance cikin shirin kallon nadin sarauta da kuma mika sandar girma ga sabon sarkin a ranar 12 ga watan Yuli.

Gwamna ya amince da nadin Oba Owolabi

Tun da fari, mun ruwaito cewa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya amince da naɗin Oba Owolabi Olakulehin a matsayin sabon sarkin ƙasar Ibadan watau Olubadan.

Kara karanta wannan

Mutuwar alkalin babbar kotun Najeriya ya jawo tsaiko a tarin shari'o'i, an samu bayanai

Makinde ya amince da naɗin sabon sarkin mai daraja biyo bayan shawarin da ya karɓa daga majalisar masarautar, wadanda aka ba ikon nada sarki.

Gwamna Makinde ya ce ya duba shawarwarin da masu nada iyayen kasa suka aiko masa kuma ya amince da wanda suka zaɓo a matsayin sabon sarkin Ibadan.

Masu nadin sarki sun zabi Oba Owolabi

A wani labarin, mun ruwaito cewa masu nadin sarki a masarautar Ibadan sun yi zama na musamman, kuma sun ayyana Oba Owolabi Olakulehin a matsayin sarkin Ibadan na gaba.

Wannan dai na zuwa ne bayan mutuwar sarkin Ibadan, Oba Lekan Balogun wanda ya yi sarauta na tsawon shekaru biyu kuma ya rasu yana da shekaru 81 a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel