Allah Ya Yiwa Tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Ibrahim Ogohi Rasuwa a Abuja

Allah Ya Yiwa Tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Ibrahim Ogohi Rasuwa a Abuja

  • An shiga jimami a Najeriya yayin da tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, dan asalin jihar Kogi, Admiral Ibrahim Ogohi ya rasu
  • Wata majiya ta ruwaito cewa Admiral Ibrahim ya rasu ne bayan shafe makwanni yana kwance a asibiti sakamakon rashin lafiya
  • An ce Admiral Ibrahim ne sojan ruwa na farko da ya fara zama babban hafsan tsaron Najeriya daga 1999 zuwa 2003 a mulkin farar hula

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, dan asalin jihar Kogi, Admiral Ibrahim Ogohi ya rasu yana da shekaru 76 a duniya.

Wata majiya daga iyalan marigayin ta ce tsohon hafsan tsaron ya rasu ne a asibiti sakamakon jinya da ya ke fama da ita.

Kara karanta wannan

Ministar Tinubu ta yi rashi, Buhari ya kadu da rasuwar da aka yi mata

Tsohon babban hafsan tsaron Najeriya ya rasu
Allah ya yi wa Admiral Ibrahim Ogohi rasuwa. Hoto: Michael Samuel Idoko
Asali: Facebook

Tsohon hafsan tsaron Najeriya ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Admiral Ibrahim ya shafe watanni a asibiti kafin rasuwarsa a gidansa na Abuja.

Majiyar ta shaidawa cewa:

"Admiral Ibrahim Ogohi ya rasu ne a safiyar ranar Lahadin nan."

Wanene Admiral Ibrahim Ogohi?

Admiral Ibrahim Ogohi CFR FSS MSS PSC, wanda aka haifa a ranar 14 ga watan Nuwamba ya kasance tsohon Admiral na sojan ruwan Najeriya ne, inji Michael Samuel Idoko daga Facebook.

Shi ne sojan ruwa na farko da ya fara zama babban hafsan tsaron Najeriya daga 1999 zuwa 2003 kuma sojan ruwa na farko da ya samu anini hudu a aikin soja a mulkin farar hula.

Marigayi Admiral Ibrahim Ogohi ya kasance kwamandan Eken NNS France a 1982, kwamanda NNS Anansa a 1985 da darakta a makarantar NDA daga 1986 zuwa 1987.

Kara karanta wannan

"Ban san Aminu Ado ba": Kwamishinan 'yan sanda ya fadi matsayarsa kan rigimar Kano

Tsohon hafsan sojin Najeriya ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon shugaban hafsan sojin Najeriya, Manjo Janar Chris Alli (mai ritaya), ya rasu yana da shekara 69 a duniya.

An ce Manjo Janar Chris Ya rike mukamin babban hafsan soji daga 1993 zuwa 1994 a karkashin mulkin Janar Sani Abacha sannan ya kasance gwamnan soja a jihar Filato.

An haifi marigayin a watan Disamban 1944, ya yi ritaya daga aikin sojan Najeriya a matsayin Manjo Janar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.