Jerin Tsofaffin Kwamishinonin Legas da Tinubu Ya Ba Manyan Mukamai a Gwamnatinsa

Jerin Tsofaffin Kwamishinonin Legas da Tinubu Ya Ba Manyan Mukamai a Gwamnatinsa

Abuja - Duk da cewa gwamnatinsa na shan suka kan zargin ya cikata da 'yan asalin Legas, Shugaba Bola Tinubu ya ba wasu tsofaffin kwamishinoni takwas manyan mukamai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Walau wannan zargin gaskiya ne ko karya, wadannan nade-naden sun fito da wani abu fili: hada kan tawagarsa da suka taka muhimmiyar rawa lokacin yana gwamnan Legas.

Jerin tsofaffin kwamishinonin Legas a gwamnatin Shugaba Tinubu
Shugaba Tinubu ya kawo wadanda suka yi aiki tare da shi a Legas zuwa gwamnatin tarayya. Hoto: @DrYemiCardoso, @officialABAT
Asali: Twitter

A rahoton da The Punch ta fitar, an tattaro jerin wasu tsofaffin ma'aikatan gwamnatin Legas da a yanzu Shugaba Tinubu ya ba su manyan mukamai a gwamnatinsa ta jam'iyyar APC.

1. Wale Edun: Ministan kudi

Wale Edun ya rike mukamin kwamishinan kudi a jihar Legas daga shekarar 1999 har zuwa 2007.

Kara karanta wannan

Gwamna ya faɗi sunan wanda ya tayar da bam, ya alaƙanta shi da ministan Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya karbi mulkin Najeriya a 2023, ya nada Edun matsayin ministan kudi da tattalin arziki.

Kafin a bashi wannan mukamin na minista, ya fara aiki ne matsayin mai ba Tinubu shawara kan tsare-tsaren kudi.

2. Olayemi Cardoso: Gwamnan CBN

Olayemi Cardoso ya shafe sama da shekara 29 a masana'antar banki, yayin da ya rike shugabancin bankin Najeriya na Citibank, daga 2010 zuwa 2022.

Cardoso ya kuma yi aiki a gwamnatin jihar Legas lokacin Tinubu yana gwamna matsayin kwamishinan tsare-tsaren tattali da kasafin kudi daga 1999 zuwa 2025.

A watan Satumbar 2023 Tinubu ya nada Cardoso matsayin gwamnan bankin CBN.

3. Dele Alake: Ministan ma'adanai

Dele Alake ya rike mukamin kwamishinan watsa labarai na jihar Kano daga 1999 zuwa 2007, mukamin da aka bashi bayan ya yi aiki matsayin mashawarci na musamman ga Tinubu.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta da shari’ar zabe ba su taka masa burki ba, an nada Abba gwarzon Gwamnoni

A watan Yunin 2023, Tinubu ya sake nada Alake matsayin mai bashi shawara kan ayyuka na musamman da sadarwa. Bayan watanni, ya nada shi ministan ma'adanai a watan Agusta.

4. Hakeem Muri-Okunola: Sakataren Tinubu

A watan Satumbar 2023, Shugaba Tinubu ya nada Muri-Okunola a matsayin babban sakatarensa na kai-da-kai. Kafin nadinsa, shi ne shugaban ma'aikatan jihar Legas.

Muri-Okunola ya yi aiki matsayin hadimin Tinubu daga 2003 zuwa 2005. Bayan wannan kuma, Tinubu ya nada shi sakataren amfani da raba filaye na jihar Legas.

5. Jide Idris: Shugaban NCDC

A watan Fabrairu, Tinubu ya nada Jide Idris a matsayin babban shugaban hukumar kula da dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC).

Idris ya kasance kwamishinan Legas na tsawon shekaru 12, inda ya yi aiki a gwamnatin Tinubu, Fashola da Ambode.

Ya kuma rike mukamin babban sakataren ma'aikatar lafiya ta jihar Legas. Idris ya maye gurbin Ifedayo Adetifa wanda ke rike da hukumar NCDC tun a watan Satumbar 2021.

Kara karanta wannan

Jihohi 3 da ke zargin gwamnatin tarayya da yi masu katsalandan

6. Dayo Mobereola: Shugaban NIMASA

A watan Maris ne dai Shugaba Tinubu ya nada Dayo Mobereola a matsayin darakta-janar na hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta Najeriya (NIMASA).

Kafin nadin nasa, Mobereola ya rike mukamin kwamishinan sufuri a Legas daga shekarar 2015 zuwa 2016.

Ya kuma yi aiki a matsayin shugaban hukumar kula da sufuri ta Lagos (LAMATA) daga 2002 zuwa 2015.

7. Olatunji Bello, Shugaban FCCPC

A ranar Litinin, 24 ga watan Yuni, Tinubu ya nada Olatunji Bello a matsayin shugaban hukumar kula da masu sayayyar kayayyaki ta Najeriya (FCCPC).

Bello ya taba rike mukamin shugaban hukumar tallace-tallace ta Jihar Legas (2010); Kwamishinan muhalli na jihar Legas (2011-2015) da sakataren gwamnatin jihar Legas (2015).

Bello ya gudanar da wadannan ayyukan ne a karkashin gwamnatocin Tinubu, Babatunde Fashola, da Akinwunmi Ambode.

8. Ayodeji Ariyo: Shugaban BPE

A cikin watan Yuni, Tinubu ya nada Ayodeji Ariyo a matsayin babban darakta na hukumar kamfanonin gwamnati (BPE).

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi magana kan yunƙurin tashin bam, ya fallasa masu ɗaukar nauyi

Daga 2013 zuwa 2015, Gbeleyi ta rike mukamin kwamishinan kudi a Legas karkashin tsohon Gwamna Fashola.

Tinubu ya amince da nadin mukamai 8

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin wasu mutane takwas a matsayin manyan sakatarori a ma’aikatun gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Nadin sababbin sakatarorin ya biyo bayan ritayar wasu daga cikin sakatarorin ma'aikatun gwamnatin tarayyar kamar yadda Ajuri Ngalale ya bayyana a wata sanarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.