An Tafka Barna Bayan Makiyaya Sun Farmaki Wasu Kauyukan Jihar Jigawa

An Tafka Barna Bayan Makiyaya Sun Farmaki Wasu Kauyukan Jihar Jigawa

  • Wasu makiyaya ɗauke da makamai sun kai hari kan wasu ƙauyuka a ƙananan hukumomi uku na jihar Jigawa
  • Rundunar ƴan sandan jihar wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin ta ce makiyayan ɗauke adduna da sanduna sun raunata mutum takwas a yayin harin
  • Makiyayan sun kuma lalata waau gonaki a hare-haren da suka kai a ƙananan hukumomin Dutse, Birnin Kudu da Kiyawa na jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da hare-haren da wasu makiyaya suka kai a wasu garuruwan jihar.

Makiyayan dai sun kai hare-haren ne a kan garuruwa da ƙauyuka huɗu a ƙananan hukumomin Birnin Kudu, Dutse da Kiyawa na jihar.

Makiyaya sun kai hari a Jigawa
Makiyaya sun raunata mutum takwas a Jigawa
Asali: Original

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Lawal Shiisu Adams ya fitar, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Katsina: An kama mutum 2 da hannu a sace mahaifiyar Dauda Kahutu Rarara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ƴan sanda suka ce kan harin makiyayan?

"Bayanai sun nuna cewa makiyaya masu yawan gaske ɗauke da kwari da baka da kibiyoyi, adduna da sanduna sun farmaki ƙauyen Baranda."
"Mutanen ƙauyen sun yi ƙoƙarin kare kansu, wanda hakan ya yi sanadiyyar raunata mutum takwas daga cikinsu. An garzaya da su babban asibitin Dutse domin kula da lafiyarsu."

- DSP Lawal Shiisu Adam

Kwamishina ƴan sanda ya kai ziyara

A cewar sanarwar, a ƙoƙarinsa na haɗa kan al’umma, magance rikice-rikice da samar da zaman lafiya a masarautar Dutse da ma jihar baki ɗaya, kwamishinan ƴan sandan jihar, Ahmed T. Abdullahi, tare da kwamandan Squadron 35PMF Dutse, sun ziyarci ƙauyukan.

Ya ce ƙauyukan da abin ya shafa su ne Kalai, Waza, Baranda da Katanga a ƙananan hukumomin Dutse, Kiyawa da Birnin Kudu, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga 100 sun kai hari kan bayin Allah, sun tafka mummunar ɓarna

Ya ƙara da cewa a rikicin da ya faru an raunata wasu mutane tare da lalata gonaki.

Ƙungiyar makiyaya ta goyi bayan Sarkin Musulmi

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta Najeriya (MACBAN) ta jaddada buƙatar da ke akwai na kare kujerar Sarkin Musulmi.

Ƙungiyar ta ce bai kamata kamata ƴan siyasa da ya kamata su yi amfani da ƙarfinsu wajen samar da shugabanci na gari ba ne za su riƙa yin wasa da kujerar Sarkin Musulmi wacce ta yi shekaru sama da 200.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng