Gwamna Na Shirin Rusa Babban Masallacin Musulmi a Jiharsa? An Gano Gaskiya

Gwamna Na Shirin Rusa Babban Masallacin Musulmi a Jiharsa? An Gano Gaskiya

  • Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya kwantar da hankulan al'ummar musulmi na garin Ilesa kan batun rusa babban masallacin garin
  • Gwamna Ademola ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta da shirin rusa masallacin saboda aikin da take yi na faɗaɗa titin hanyar Ilesa
  • A cikin wata sanarwa da mai magana da gawun gwamnan ya fitar, ya ba da tabbacin cewa wani ɓangare kawai za a taɓa ba ainihin ginin masallacin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke ya yi magana kan raɗe-raɗin da aka yi kan batun rusa babban masallacin Ilesa a jihar.

Gwamna Ademola Adeleke ya ba al’ummar Musulmin Ilesa cewa babu wani shiri na rusa masallacin Ilesa, sakamakon aikin faɗaɗa titin Ilesa.

Kara karanta wannan

"NLC ta yi ƙarya," Gwamna ya fara biyan N40,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamna Ademola Adeleke ya ce bai da shirin rusa masallaci a Osun
Gwamna Ademola Adeleke ya musanta batun rusa masallacin Ilesa Hoto: @AAdeleke_01
Asali: Twitter

Gwamna Adeleke ya ce alƙawarin da ya yi na ba zai rusa masallacin ba har yanzu yana nan daram, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mallam Olawale Rasheed ya fitar a Osogbo, babban birnin jihar, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

"Gwamna Adeleke ya karɓi roƙon shugabannin Musulmi na Ilesa sannan ya ba da umarnin a ba da sabon tabbaci cewa ba za a rushe masallacin ba sakamakon aikin faɗaɗa titin hanyar da ake yi."
"Al'ummar musulmi kada su ji wani tsoro domin ba za a taɓa masallacin ba. Kawai wani daga cikin ɓangaren masallacin ne da ya fito za a taɓa ba ainihin ginin ba kamar yadda aka nuna da farko."
"Gwamnan ya kuma umarci jami'an ma'aikatar ayyuka da samar da ababen more rayuwa su tattauna da shugabannin musulmi kan lamarin."

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi magana kan yunƙurin tashin bam, ya fallasa masu ɗaukar nauyi

- Mallam Olawale Rasheed

Kotu ta ɗaure na kusa da Gwamna Adeleke

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotu ta umarci a tsare makusancin Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, Olalekan Oyeyemi, a gidan gyaran hali kan zargin ta'addanci da kisan kai.

Kotun ta umarci a garƙame hadimin gwamnan a kurkukun Ile-Ife bisa tuhumar da ta shafi ta'addanci da kisan mutum huɗu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel