NDPHC: Shugaban Najeriya Ya Zabi Wasu Gwamnonin Jihohi Ya Raba Masu Mukami a Gwamnatinsa
- Shekara guda da shiga ofis, Dikko Umar Radda ya samu mukami a gwamnatin tarayya kamar yadda sanarwa ta zo
- Ibrahim Kaula Mohammed ya shaidawa duniya cewa mai gidansa ya samu kujera a majalisar gudanarwar NDPHC
- NEC ta yarda Dikko Radda da wasu gwamnonin jihohi biyar su kula da sha’anin kamfanin wutar lantarki na Neja Delta
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Katsina - Gwamna Malam Dikko Umar Radda ya samu mukami a gwamnatin tarayya bayan sahalewar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Bola Ahmed Tinubu ya nada gwamnan Katsina a cikin majalisar gudanar da harkokin kamfanin wutar lantarki na Neja Delta (NDPHC).
Dikko Radda ya samu matsayi a NDPHC
Sanarwar da gwamnatin jihar Katsina ta fitar a shafinta na X ya bayyana cewa majalisar NEC mai kula da tattalin arziki ta amince da nadin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakataren yada labaran gwamnatin jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed ya ce Dikko Radda yana cikin gwamnoni shida da aka zaba.
Gwamnoni sun shiga majalisar NDPHC
Ana zakulo gwamnonin da za su sa ido a aikin hukumar ta NDPHC ne daga duka bangarorin Najeriya domin ganin an kamanta adalci.
Sauran ‘yan kwamitin sun kunshi Mai girma Farfesa Babagana Zulum na jihar Borno da gwamnan jihar Ekiti watau Mista Biodun Oyebanji.
Tinubu ya nada Hope Uzodimma wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC da kuma shugaban NGF na kasa, Abdulrahman Abdulrazaq.
Sanarwar fadar shugaban kasa ta nuna wani gwamna da ya shiga wannan majalisa shi ne na jihar Akwa Ibom watau Mai girma Fasto Umo Eno.
Radda, Eno za su zauna da Uzodinma
Legit Hausa ta lura a cikin jerin gwamnonin da aka zaba su wakilci takwarorinsu a NDPHC, Radda da Umo Eno ne kadai sababbin shiga.
Ibrahim Kaula Mohammed ya rahoto gwamnan na Katsina ya na mai farin ciki da wannan mukami, yake cewa zai yi bakin kokarinsa.
Sanarwar ta ce Radda zai kawo gogewarsa a majalisar tare da ba da gudumuwa wajen ganin an biya bukatar Arewa maso yammacin kasar.
Bola Tinubu ya yi nadin mukamai
Labarin da muka samu shi ne Bola Tinubu ya ba Mahmood Fatima Sugra Tabi'a da Danjuma Mohammed Sanusi mukami a gwamnatin tarayya.
Tinubu ya amince Isokpunwu Christopher Osaruwanmwen, Keshinro Maryam Ismaila da Akujobi Chinyere Ijeoma su zama sakataren din-din-din.
Asali: Legit.ng