Za a Sha Jar Miya: Tinubu Zai Fara Biyan Tallafin N150bn Ga ’Yan Kasa, Jama’a Za Su Caba

Za a Sha Jar Miya: Tinubu Zai Fara Biyan Tallafin N150bn Ga ’Yan Kasa, Jama’a Za Su Caba

  • Gwamnatin Tarayya ta fadi ranar fara biyan tallafin bashi har N150bn ga masu kananan sana'o'i da 'yan kasuwa
  • Ministar masana'antu da kasuwaci, Doris Uzoka-Anite ta tabbatar da cewa a karshen watan Yulin 2024 za a fara biya
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani wanda ya cike tallafin kuma dan kasuwa kan sanarwar da gwamnatin ta fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sanya ranar raba bashin N150bn ga kananan 'yan kasuwa da masu sana'o'i.

Gwamnatin Bola Tinubu ta bayyana haka ne a jiya Alhamis 27 ga watan Yunin 2024 a birnin Tarayya Abuja.

Tinubu ya shirya biyan tallafin N150bn ga 'yan Najeriya
Bola Tinubu ya shirya fara biyan tallafin N150bn a karshen watan Yulin 2024. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Tinubu ya shirya biyan tallafin N150bn

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ministar masana'antu da kasuwanci, Doris Uzoka-Anite ita ta tabbatar a shafin X.

Kara karanta wannan

Kano: Masallata sun rasa ransu bayan tirela ta bi kansu ana tsaka da jam'in Juma'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uzoka-Anite ta tabbatar da cewa zuwa karshen watan Yulin 2024 za a fara biyan kudin ga wadanda suka cika ka'ida.

Ta ce 60% na kudin an raba su ga 'yan kasar inda suka samu N50,000 a kananan hukumomi 774 na kasar kyauta ba bashi ba.

A watan Disambar 2023 ne Tinubu ya kaddamar da tallafin domin taimakawa masu kananan sana'o'i da 'yan kasuwa.

Yadda Tinubu ya kasafta kudin tallafin

Daga cikin kudin da aka ware na N150bn, an tura N75bn ga masu kananan sana'o'i da kuma N75bn ga masana'antu.

"Wadanda suka cike talafin nan har yanzu ba mu biya ba, muna kara gode muku kan irin hakuri da kuke yi."
"Ana ci gaba da biya saboda mun ware 60% na kudin a kananan hukumomi 774 da muke da su."
"Kowa zai iya bibiyar wadanda suka ci gajiyar a kananan hukumomi ta wannan yanar gizo: grant.fedgrantandloan.gov.ng/learning/dis."

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta dauko tallafi da ayyukan inganta rayuwar 'yan kasa

Hirar Legit Hausa ta wani dan kasuwa

Legit Hausa ta ji ta bakin wani wanda ya cike tallafin kuma dan kasuwa kan sanarwar da gwamnatin ta fitar

Abubakar Umar mai harkar magani ya ce sun cike tuntuni amma har yanzu dai babu komai sai gashi an sanar da za a fara biya.

Ya ce tabbas hakan zai taimaka musu wurin inganta harkokin kasuwancinsu duba da yadda tattalin arziki ya rikice.

Tinubu zai kuma ba da sabon tallafi

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da tallafawa gidaje miliyan 3.6 a yankunan da ke fadin Najeriya guda shida.

Tinubu ya tabbatar da cewa akalla gidaje akalla N50,000 ne zuwa N100,000 za su samu wannan tallafi na tsawon watanni uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel