Bayan Neman Taimako, Sanusi II Ya Gwangwaje Dattijo da Makudan Kudi a Bidiyo
- Wani dattijo ya barke da murna bayan neman taimakon kudi domin lalacewar wani bangare na gidansa a Kano
- Dattijon ya samu gudunmawar kudi har N200,000 daga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II kan lamarin
- An gano dattijon a cikin faifan bidiyo a fadar Sarki yana godiya tare da kora ruwan addu'o'i ga Muhammadu Sanusi II
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya taimakwa wani dattijo da makudan kudi a jihar.
Sanusi ya tallafawa dattijon da kudi N200,000 bayan ya nemi alfarma kan rushewar wani bangaren gidansa.
Kano: Sanusi II ya taimaki wani dattijo
Masarautar Kano ta wallafa faifan bidiyon inda dattijon ke godiya a fada a shafin X a yau Juma'a 28 ga watan Yunin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin ya mika wannan kyauta ce ta hannun Falakin Kano domin ya samu damar gyara bangaren gidan nasa.
Dattijon ya yi godiya ga Sanusi II
"Ina godiya sosai naga kudi, taimakon da na nema gida na ya lalace an dauki kudi har N200,000 aka bani."
"Ina matukar godiya, Allah ya raba ka da makiya ya taimake ke."
- Cewar dattijon
Daga bisani dattijon ya kora ruwan addu'o'i ga sarkin domin gudanar da mulkinsa cikin nasara ba tare da matsala ba.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar jihar Kano tun a karshen watan Mayun 2024.
Hakan ya biyo bayan tube Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga sarautar tare da mayar da Muhamamdu Sanusi II kan kujerar ba tare da wani bata lokaci ba.
Masu tafsiri sun ziyarci Sanusi II
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar mata masu tafsirin Alkur'ani mai girma ta ziyarci fadan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Kungiyar ta kai caffan ban girma domin nuna goyon baya ga sarkin inda mambobin suka kora ruwan addu'o'i ga sarkin.
Sarkin a martaninsa, ya yi musu godiya inda ya kara musu karfin guiwar ci gaba da ayyukan alheri da suke yi na Musulunci.
Asali: Legit.ng