“Siyasa Ce Kawai”: NNPP Ta Kalubalanci EFCC Kan Binciken Kwankwaso, Ta Nemi Hujjoji

“Siyasa Ce Kawai”: NNPP Ta Kalubalanci EFCC Kan Binciken Kwankwaso, Ta Nemi Hujjoji

  • Jam'iyyar NNPP ta kalubalanci hukumar EFCC kan binciken Sanata Rabiu Kwankwaso ba tare da hujjoji ba
  • Shugaban matasa na jam'iyyar, Auwal Musa shi ya bayyana haka inda ya ce mene ya saka sai yanzu ake bincikensa
  • Ya kalubalance su kan binciken hazikin mutum mai kokari inda ya ce ya kamata su je Kano su ga ayyukan da ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP ta yi martani kan binciken da hukumar EFCC ke yiwa Sanata Rabiu Kwankwaso.

Shugaban matasan jam'iyyar, Auwal Musa ya bayyana tuhumar a matsayin bita da kullim siyasa kawai da ake masa.

NNPP ta magantu kan binciken Kwankwaso da hukumar EFCC ke yi
Jam'iyyar NNPP soki hukumar EFCC kan binciken Rabiu kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Economic and Financial Crimes Commission.
Asali: UGC

Kwankwaso: NNPP ta kalubalanci hukumar EFCC

Auwal Musa ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 27 ga watan Yunin 2024 a Kaduna inda ya ce ana neman bata sunan Kwankwaso, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Yayin da ake rade radin tuge shi, Sultan ya tura sako ga rundunar sojoji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Auwal ya kalubalanci hukumar da ta kawo hujjoji saboda kare kanta daga zargin bita da kullin siyasa, TheCable ta tattaro.

"Ina kalubalantar hukumar EFCC da ta fitar da hujjoji domin tabbatar da tuhumar da take yi kan Rabiu Kwankwaso."
"Idan har ba ta kawo hujjoji kan zarginsa da take yi ba, to neman bata masa suna take da bita da kullin siyasa."
"Mene dalilin da ya saka sai yanzu aka fara bincikensa bayan shafe shekaru tara da barinsa mulki?."

- Auwal Musa

NNPP ta shawarci EFCC game da Kwankwaso

Auwal ya kalubalance ta kan bincikar mutum mai hazaka irin Rabiu Kwankwaso da cewa bata lokacinta kawai take yi.

Auwala ya bukaci hukumar EFCC ta yi fatali da duk wani korafi da wani dan siyasa ko wasu tsairaru suka yi kan Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Mutuwar jami’in Kwastam: Shugaba Tinubu ya aikawa Iiyalin Marigayi Etop Essien saƙo

Rabiu Kwankwaso ya shigar da EFCC kara

Kun ji cewa Babbar Kotun jihar Kano da ke zamanta a Audu Baƙo za ta fara zaman sauraron ƙorafin da Rabiu Musa Kwankwaso da wasu mutum bakwai suka shigar da EFCC.

Jagoran NNPP da sauran mutanen su bakwai sun maka hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC a gaban kotun ne kan abin da ya shafi tauye haƙƙinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel