Tsige Sarkin Musulmi: An Bayyana Hanyar da Za a Takawa Gwamnatin Sokoto Burki

Tsige Sarkin Musulmi: An Bayyana Hanyar da Za a Takawa Gwamnatin Sokoto Burki

  • Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta sake magana kan zargin yunkurin da gwamnatin Sokoto ke yi na tsige Sarkin Musulmi
  • Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Lakin Akintola ya bayyana yadda tsige Sultan zai shafi dukkan al'ummar Musulmi a Najeriya
  • Ishaq Lakin Akintola ya kuma fadi hanya da za a bi wajen kare martabar mai alfarma Sarkin Musulmi daga gwamnatin Sokoto

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Lakin Akintola ya kara bayani kan zargin yunkurin tsige mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III.

Farfesa Ishaq Lakin Akintola ya ce martanin da gwamnatin Sokoto ta yi na cewa ba za ta tsige Sultan ba, ba mai gamsarwa ba ne.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: ASUU ta fadi matakin da ta dauka bayan ganawarta da gwamnatin tarayya

Sarkin Musulmi
MURIC ta kawo mafita kan tsige sarkin Musulmi. Hoto: Ahmad Aliyu|Daular Usmaniyya
Asali: Facebook

Farfesa Ishaq Lakin Akintola ya yi bayanin ne a cikin wata hira da ya yi da jaridar Daily Trust kan batun tsige Sarkin Musulmi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

MURIC da alamun tsige Sarkin Musulmi

Farfesa Ishaq Lakin Akintola ya ce gwamnonin da suka gabata a jihar Sokoto suna da alaka mai kyau da Sarkin Musulmi.

Ya ce gwamnatin yanzu ta nuna alamu da suke ishara da cewa za ta iya sauke Sarkin Musulmi musamman wajen rage masa karfi da rashin tarayya da shi cikin lamura.

"Tsige Sultan babban al'amari ne" - MURIC

Shugaban na MURIC ya ce maganar tsige Sarkin Musulmi abu ne da zai shafi dukkan al'ummar Musulmi a Najeriya.

Saboda haka bai kamata gwamnan jiha daya ya aikata abin da zai baƙantawa dukkan Musulmin Nijeriya ba.

An kawo mafita kan taba Sarkin Musulmi

Farfesa Akintola ya ce yana kira da majalisar jihar Sokoto da ta soke dokar da ta ba gwamantin jihar damar sauke Sarkin Musulmi, kamar yadda ya wallafa a shafinsa.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta da shari’ar zabe ba su taka masa burki ba, an nada Abba gwarzon Gwamnoni

Ya kara da cewa wannar ita ce hanya daya da za a bi wajen magance barazanar da gwamnatin ke yi ga mai alfarma Sarkin Musulmi.

Atiku ya yi magana kan raina masarautu

A wani rahoton, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya yi kira da a sanya masarautu a cikin kundin tsarin mulki.

Atiku Abubakar ya ce hakan ne zai kare masarautu daga barazanar rugujewa saboda katsalandan da gwamnoni ke yi wa sarakuna a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel