Sabon Mafi Ƙarancin Albashi: Gwamnoni 17 Sun Aikawa Tinubu Muhimmiyar Buƙata

Sabon Mafi Ƙarancin Albashi: Gwamnoni 17 Sun Aikawa Tinubu Muhimmiyar Buƙata

  • Gwamnoni 17 na kungiyar gwamnonin kudancin Najeriya sun yanke shawarar bunkasa samar da wutar lantarki a jihohinsu
  • A wani rahoto da ke yawo a ranar Alhamis, gwamnonin sun yanke shawarar samar da 90,000MW na lantarki a shiyyar
  • Gwamnonin sun kuma aika sako ga Shugaba Bola Tinubu kan mafi ƙarancin albashi da ake ci gaba da tattaunawa da kungiyoyin kwadago

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Ogun - Kungiyar gwamnoni 17 na Kudu maso Yamma, Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu sun nemi a bar kowace jiha ta biya albashi gwargwadon karfin tattalin arzikinta.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar bayan taro da kungiyar gwamnonin ta fitar jim kaɗan bayan ganawarsu a Abeokuta, jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta da shari’ar zabe ba su taka masa burki ba, an nada Abba gwarzon Gwamnoni

Gwamnonin Kudu sun yi magana kan sabon mafi ƙarancin albashi
Gwamnoni 17 sun nemi Tinubu ya bar jihohi sun yanke sabon albashi. Hoto: @jidesanwoolu
Asali: Twitter

Matsayar gwamnonin Kudu kan karin albashi

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito gwamnonin sun nemi gwamnatin Bola Tinubu ta bar gwamnoni su tattauna da kungiyoyin kwadago na jihohinsu domin cimma matsaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar da take dauke da sa hannun dukkanin gwamnonin 17 ta ce hakan ne zai sa a samu daidaito tsakanin ma'aikata da gwamnatin jihohi.

Gwamnoni 17 sun shirya samar da lantarki

Sanarwar ta kara da cewa gwamnonin shiyyar Kudu sun bayyana shirinsu na samar da akalla 90,000 MW na wutar lantarki domin amfanin sama da mutane miliyan 90 na shiyyar.

Kungiyar ta yi amfani da dabarar samar da 1,000 MW na lantarki domin amfanin mutane miliyan daya a cewar rahoton Vanguard.

Kungiyar ta ce za ta yi amfani da sabuwar dokar da ta ba jihohi damar samar da nasu wutar lantarkin wajen ganin an inganta samar da wutar a shiyyar Kudancin kasar.

Kara karanta wannan

"Kowa ya yi abin da zai iya": Kungiyar gwamnoni ta fitar da matsaya kan karin albashi

Jigon PDP ya magantu kan sabon albashi

A wani labarin, mun ruwaito wani jigon jam'iyyar PDP, Rilwan Olanrewaju ya ce gwamnoni na da karfin ikon biyan sama da N100,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

A wata tattaunawa da Legit.ng, Mista Rilwan Olanrewaju ya ce duk da hakan, akwai bukatar a bar jihohi su biya abin da za su iya gwargwadon kudin da suka iya samu a kowanne wata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel