Mummunan Gobarar Dare Ta Tashi a Kasuwar Abuja, an Gargadi Mazauna Yankin Karu

Mummunan Gobarar Dare Ta Tashi a Kasuwar Abuja, an Gargadi Mazauna Yankin Karu

  • A yammacin yau Alhamis, 27 ga watan Yunin 2024 ne gobara ta tashi a babbar kasuwar Karu da ke babban birnin tarayya Abuja
  • An ruwaito cewa gobarar ta kama gadan-gadan yayin da jami'an hukumar kwana-kwana ke iya bakin kokarinsu domin shawo kanta
  • Wani bidiyo ya nuna yadda gobarar take ci a kasuwar inda aka yi kira ga mazauna yankin da su guji taruwa a wajen da wutar ta tashi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rahotanni da ke shigo mana yanzu na nuni da cewa wuta ta kama a kasuwar Karu da ke babban birnin tarayya Abuja, inda take ci har yanzu.

Gobarar wadda ta tashi a yammacin ranar Alhamis, ta mamaye shaguna da dama yayin da take ci gadan-gadan.

Kara karanta wannan

Ruwa ya cinye wasu dalibai a hanyarsu ta dawo wa daga jarrabawa a Kaduna

Abuja: A halin yanzu kasuwar Karu na ci da wuta.
Gobara ta tashi a kasuwar Karu da ke Abuja. Hoto: @Fedfireng
Asali: Facebook

Gobara ta tashi a kasuwar Karu, Abuja

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa har zuwa karfe 8:00 na dare jami'an hukumar kashe gobara na kokarin shawo kan wutar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ganau ya shaida cewa an kira jami'an hukumar kwana-kwana domin ganin gobarar ba ta tsallaka gidajen makota ba.

Har zuwa yanzu dai ba a gano musabbabin tashin wutar ba yayin da hukumomi ke kira ga mazauna yankin da su guji taruwa a inda wutar ta tashi.

A cewar wani bidiyo da @Abujaplug ya wallafa a shafinsa na X, ya ce "kasuwar Kauru ta kama da wuta."

Kalli bidiyon a ƙasa:

Gobara ta tashi a kasuwar Adamawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa gobara ta tashi a wata kasuwar karamar hukumar Yola ta Kudu, jihar Adamawa, inda ta lalata shaguna masu yawa.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta dauki mataki bayan Tinubu ya yi biris da maganar ƙarin albashi

An ruwaito cewa mataimakiyar gwamnan jihar Adamawa, Farfesa Kaletapwa Farauta ta ziyarci kasuwar da wutar ta tashi a ranar Litinin.

Mataimakiyar gwamnan ta jajantawa 'yan kasuwar bisa wannan iftila'in da ya fada masu tare da ba su tabbacin cewa gwamnati za ta tallafa masu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel