Rikici Ya Kaure Tsakanin Masu Nadin Sarauta, An Shafe Shekaru 4 Babu Sarki
- Masu nadin Sarki a yankin Ifon da ke karamar hukumar Ose a Ondo sun koka kan yadda ake kokarin ƙaƙaba musu wani a matsayin sarki
- Sakatarensu, Kehinde Falowo ya tabbatar da haka a yau Alhamis 27 ga watan Yunin 2024 inda ya zargi wasu ƴan siyasa da katsaladan
- Wannan na zuwa ne yayin da rikici ya barke a tsakaninsu da rarrabuwar kawuna kan wanda zai kasance sarkin yankin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Rikici ya barke tsakanin masu nadin sarki a kauyen Ifon da ke karamar hukumar Ose a jihar Ondo.
Hakan ya biyo bayan rarrabuwar kawuna tsakanin masu nadin sauratar kan wanda ya kamata a nada sarki a yankin.
An zargi ƴan siyasa da kawo rikicin sarauta
Wani tsagi na masu nadin sarki sun zargi kokarin tilasta musu Prince Adelanke Odogiyon a matsayin Sarki, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren masu nadin Sarkin, Kehinde Falowo ya fitar a ya Alhamis 27 ga watan Yunin 2024.
Sun zargi wasu daga mukarraban gwamnati da neman kakaba musu Odogiyon domin biyan buƙatar kansu, Tribune ta tattaro.
Daya daga cikin masu nadin Sarkin ya gargadi masu zargin da su guji neman batawa gwamnatin jihar suna kan wannan rigima.
Ondo: An shafe shekaru 4 babu Sarki
Kujerar sarautar ta kasance babu kowa tun bayan rasuwar Oba Israel Adeusi a watan Nuwamban 2020 bayan shafa shekaru 23 a kanta.
Tun wancan lokaci har zuwa yanzu al'ummar yankin ta gaza yanke hukuncin wanda za a daura ya maye gurbin marigayin.
Kotu ta rusa sababbin ƙananan hukumomin Ondo
A wani labarin, kun ji cewa wata Babbar Kotun jihar Ondo da ke zama a Akure ta rusa dokar da marigayi Oluwarotimi Akeredolu ya zartar na kirkirar karin kananan hukumomi 33.
Alkalin kotun Mai Shari'a, Adegboyega Adebusoye ya yanke wannan hukuncin a ranar Alhamis 20 ga watan Yunin 2024 da muke ciki.
Adegboyega Adebusoye ya ayyana kirkirar kananan hukumomin a matsayin abin da ya sabawa kundin tsarin mulki kuma ya sabawa ka’ida.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng