NAFDAC ta Tattaro Jabun Magunguna a Yankin Arewa, An Bankawa Kayan Miliyoyi Wuta
- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta gano tarin magunguna da kayan abinci na jabu a jihohin da ake Arewa maso Yamma
- Darakta janar ta hukumar, Mojisola Adeyeye ta bayyana cewa an kona jabun kayayyakin a Kano domin inganta lafiyar al'umma da bunkasa tattalin arziki
- Daga kayayyakin da aka kona akwai magunguna da jabu da wadanda wa'adin amfaninsu ya kare, sai kayan kwalliya da magungunan kwari
Kano - Hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta tattaro jabun kayayyaki daga Arewa maso Yamma na kasar nan da suka tasamma miliyoyin Naira.
Daga cikin kayan da aka kona akwai wadanda wa'adin amfaninsu ya kare, yayin da wasu cikinsu na jabu ne da sauran gurbatattun kaya ga lafiyar dan Adam.
Jaridar The Nation ta wallafa cewa bayan tattaro kayan da kudinsu ya kai N985m, an kona su kurmus domin kar ci gaba da sayar da su a kasuwanni.
NAFDAC ta cire jabun maganguna a gari
Hukumar kula da inganci abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta ce kona kayan jabu da marasa inganci da ta yi a Kano zai taimakawa lafiyar al'umma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Darakta janar ta hukumar, Mojisola Christianah Adeyeye ce ta bayyana haka lokacin da aka kona jabun magunguna a jihar Kano, kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.
“Kuma tun da jiki mai lafiya zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki, (kona magungunan) zai taimaka wajen samun karuwar arziki."
- Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye
Daga cikin kayan da aka kona akwai magunguna, kayan kwalliya da shafe-shafe, magungunan kwari da na amfani a gonaki.
Ta bayyana cewa an kona kayayyakin a wajen jihar Kano domin kare lafiyar jama'a.
NAFDAC ta gargadi masu shafa man 'bilicin'
A baya mun kawo labarin cewa hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta gargadi mata masu amfani da man kara hasken fata a fadin kasar nan. Hukumar, ta sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce man kara hasken fata na 'Caro White' na illa sosai da fatar dan Adam.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng