Shigar Banza: An Kori Mataimakiyar Shugaban Masu Rinjaye Daga Zauren Majalisar Edo
- An kwashi 'yan kallo a zauren majalisar dokokin jihar Edo a ranar Laraba, bayan da aka kori wata 'yar majalisa saboda ta yi shigar banza
- An ruwaito cewa kakakin majalisar, Blessing Agbebaku ta umarci mataimakiyar shugaban masu rinjaye da ta fice daga zauren majalisar
- Hon. Nicholas Asonsere ne ya gabatar da korafi gaban zauren majalisar kan shigar tsiraici da 'yar majalisar ta yi wanda ya ce ya sabawa ƙa'ida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Edo - A jiya Laraba ne aka kori mataimakiyar shugaban masu rinjaye ta majalisar Edo, Natasha Osawaru daga zauren majalisar saboda ta yi shigar banza.
Kakakin majalisar Edo, Blessing Agbebaku ta umarci Osawaru, mai wakiltar mazabar Egor da ta fice daga zauren majalisar bayan dan majalisa Nicholas Asonsere ya gabatar da korafi.
'Yar majalisa ta yi shigar banza a Edo
Hon. Asonsere mai wakiltar Ikpoba-Okha ya yi nuni da cewa shigar da mataimakiyar shugaban masu rinjayen ta yi ya sabawa dokar majalisar, inji jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan majalisar ya ce:
"Wannan zauren majalisar wani wuri ne mai tsarki wanda ba za mu amince wasu su rika yin abubuwan da basu dace ba a ciki.
"Mun jima muna kawar da kai daga wasu munanan dabi'u na 'yan majalisar mu, ya zama wajibi mu yiwa tufkar hanci tun yanzu."
"A hukunta masu karya doka" - Asonsere
Jaridar PM News ta ruwaito ɗan majalisar ya nemi izinin kakakin majalisar domin zayyana kadan daga cikin dokokin zauren majalisar.
Ya ce majalisar na da na da 'Bible' din wanda take kallo a matsayin kundin dokar gudanarwar majalisar jihar Edo.
"Duk wani mamba da ya karya dokokin da ke cikin wannan littafi, dole ne a hukunta shi bisa turbar doka."
- Inji Hon. Asonsere.
Majalisar dattawa ta amince da bukatar Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar dattawa ta amince da bukatar Shugaba Bola Tinubu na tsawaita wa'adin aiwatar da kasafin kudin 2023.
Majalisar ta amince za a ci gaba da amfani da kasafin 2023 tare da karin kasafin shekarar har zuwa ranar 30 ga watan Disambar 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng