Shigar banza: Jama’a sun yi caa akan wata budurwa, ta sha da kyar

Shigar banza: Jama’a sun yi caa akan wata budurwa, ta sha da kyar

- Wata mata ta sha da kyar a hannun wasu matasa

- lamarin ya faru ne sakamakon budurwar tayi shigar banza

Wata mata da ba’a bayyana sunanta har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ta sha da kyar a hannun wasu matasa da suka fusata su kayi kanta a kasuwar Wuse dake Abuja.

Legit.ng ta ruwaito lamarin ya faru ne sakamakon budurwar tayi shigar banza, inda ta daura dan kamfai a kugunta, luma lamarin ya auku ne a daidai lokacin da take kokarin shiga kasuwa Wuse.

KU KARANTA: Watan Ramadana: Kwankwaso yayi rabon shinkafa

Kamar yadda wani ma’abocin Tuwita @Manipeters ya gani da idanunsa, yace matasan sun yi yunkurin yi ma budurwar tsirara ne, sai dai an samu wani direban Tasi da yayi karfin hali ya cece ta.

Shigar banza: Jama’a sun yi caa akan wata budurwa, ta sha da kyar
Budurwar

Shi wannan direba zuwa yayi da motarsa, ya kara kusa da matar, sa’annan ya bude mata kofa, inda nan da nan tayi wuf ta shige, a haka ta tsira.

Sai dai duk da wannan namijin kokari da wannan mutumi yayi, sai da matasan su kayi kokarin bude motar da niyyar fito da budurwar, amma aka samu wasu masu hankali suka hana su, daga nan sai direban ya tafi da ita.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel