Kudin Wuta: KEDCO ya Maka Kungiyar da Yake Zargi da Jawo Masa Asarar Biliyoyi a Kotu

Kudin Wuta: KEDCO ya Maka Kungiyar da Yake Zargi da Jawo Masa Asarar Biliyoyi a Kotu

  • Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya garzaya kotu ya na tuhumar kungiyar masu sarrafa kaya ta Najeriya
  • KEDCO na karar MAN ne bisa zargin jawo masu dimbin asarar da ta kai N5bn saboda kin biyan sabon kudin wuta da aka kara
  • Hukumar kula da rarraba hasken wutar lantarki na NERC ta amince da kara kudin wuta da ake karba daga wasu abokan hulda

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki KEDCO ya maka kungiyar masu sarrafa kayan abinci na kasa (MAN) gaban kotun babbar tarayya da ke Abuja.

Kamfanin na zargin kungiyar da shigar masu aiki da har ta kai sun tafka mummunar asarar N5.3bn a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Kotu ta tasa keyar 'Sanata' zuwa kurkuku saboda zargin damfarar 'yar kasar waje

KEDCO
KEDCO ta kai MAN kotu Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Punch News ta wallafa cewa KEDCO ya dauki matakin ne bayan kungiyar MAN ta ki amincewa da biyan karin kudin wuta da su ka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"MAN ta jawo mana asara," KEDCO

Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya bayyana cewa kin biyan sabon kudin wuta da aka yanke ya jawo asarar N5.3bn a duk wata.

Sun dora laifin hakan kan hukuncin kotu da kungiyar masu sarrafa kayyaki ta kasa ta samo ya dakatar da biyan sabon kudin.

Daily Trust ta wallafa cewa ayyukan kamfanin ya jawo mata asara mai dimbin yawa da kai biliyoyin Naira duk wata.

Shugaban sashen yada labarai na KEDCO, Sani Bala Sani ya ce matakin da MAN ta dauka ya tauye mata hanyoyin samun kudi.

Kotu: An dakatar da karbar kudin wuta

A wani rahoton kun ji cewa wata babbar kotu a Kano ta dakatar karbar sabon kudin wuta da hukumomi su ka kara ga 'yan kasar nan.

Kara karanta wannan

Ruwa ya cinye wasu dalibai a hanyarsu ta dawo wa daga jarrabawa a Kaduna

Kamfanonin da su ka shigar da kara sun hada da Supper Sack Limited, BBY Sack Limited, Mama Sannu Industries Limited, Dala Good Nigeria, Tofa Textile da Manufacturers Association of Nigeria.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel