Shettima Ya Sa Labule da Gwamnoni Kan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi da Wasu Batutuwa
- Ssnata Kashim Shettima da gwamnoni sun sa labule a fadar shugaban kasa da ke Abuja kan muhimman batutuwa
- Mataimakin shugaban ƙasar ne ke jagorantar taron wanda ke gudana karkashin majalisar tattalin arzikin ƙasa (NEC)
- Ana sa ran taron zai tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arziƙi da kuma sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, gwamnonin jihohi da wasu 'yan majalisar tattalin arziki (NEC) sun shiga taro yanzu haka a Aso Villa.
Wannan taro na majalisar tattalin arziki na zuwa ne kwanki ƙalilan bayan majalisar zartaswa ta ɗage tattaunawa kan batun mafi ƙarancin albashi.
NLC: Yadda ake kai kawo kan ƙarin albashi
Ministan yada labaru, Muhammad Idris, ya ce jingine batun ya zama wajibi domin Shugaba Tinubu ya kara tuntubar sauran masu ruwa da tsaki kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana sa ran NEC za ta tattauna kan batun ƙarin albashin kuma mai yiwiwa ta cimma matsaya da ɗaukar mataki na gaba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A daren jiya ma kungiyar gwamnonin Najeriya suka yi taro a Abuja inda suka tattauna kan sabon mafi karancin albashi da wasu batutuwan da suka shafi ƙasa.
Sanarwar bayan taron ta ce Gwamnonin sun amince da, "ci gaba da tuntuɓar masu ruwa da tsaki don cimma matsayar da ta dace."
Mambobin majalisar tattalin arzikin sun hada da gwamnonin jihohi 36, da gwamnan babban bankin kasa (CBN) da sauran waɗanda aka naɗa.
Gwamnonin da suka halarci taron karin albashi
Mataimakin shugaban kasa ne ke jagorantar majalisar kuma suna taro kowane wata don bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tattalin arziki, Leadership ta ruwaito.
Gwamnonin da suka halarci taron karo na 141 da ke gudana yanzu haka sun haɗa da Usman Ododo (Kogi), Uba Sani (Kaduna), Lawal Dauda (Zamfara), da Charles Soludo (Anambra).
Sauran sun kunshi Seyi Makinde, (Oyo), Lucky Ayedatiwa, (Ondo) Abdullahi Sule, (Nasarawa), AbdulRahman AbdulRazaq (Kwara), Caleb Mutfwang, (Plateau), Hope Uzodimma (Imo) da Biodun Oyebanji (Ekiti).
Har ila yau akwai Muhammed Inuwa Yahaya, (Gombe), Peter Mbah, (Enugu), Francis Nwifuru (Ebonyi), Dapo Abiodun, (Ogun), Umar Radda, (Katsina), Abba Yusuf (Kano), Umar Namadi, (Jigawa) da Umar Bago, (Niger) sun halarci taron.
NLC ta mayar da martani ga Tinubu
A wani rahoton Kungiyar kwadago ta nuna rashin jin dadi kan yadda shugaban kasa Bola Tinubu ya yi watsi da maganar ƙarin albashin ma'aikata.
A sanadiyyar haka, 'yan kwadago sun dauki mataki domin duba abin da ya kamata su yi a gaba domin neman hakkin ma'aikata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng